Afirka ta Kudu: ’Yan fashi sun daba ma dan Najeriya wuka har ya mutu

Afirka ta Kudu: ’Yan fashi sun daba ma dan Najeriya wuka har ya mutu

- ’Yan fashi sun daba ma dan Najeriya wuka har ya mutu

- Hare-haren da ake kai ma ‘yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu sunyi muni

Shugaban kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu (NICASA), Ben Okoli, yace wani dan Najeriya mai suna Mr Okechukwu Henry, dan asalin jihar Imo ya hadu da ajalinsa sakamakon wukar da ‘yan fashin da ba a san ko su wane ba suka daba masa.

Shugaban na NICASA ya bayyana hakan a wata wasikar da ya aika ma jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu Kuma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya samu kofen wasikar a ranar Jumu’ 3 ga watan Mayu a Abuja.

Okoli yace kungiyarsu ta gaji da aiko da gawarwakin ‘yan Najeriya da suke rasa rayukkansu daga ta’addancin da ake kitsa masu a kasar ta Afirka ta Kudu.

“Wata musiba ta sake fada wa al’ummar ‘yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu, a ranar Jumu’a 3 ga watan Mayu, da misalin karfe hudu na yamma lokacin da wasu ‘yan fashi ‘yan asalin Afirka ta Kudu suka daba masa wuka.

“Marigayi Henry, dila ne da ya kware wurin sana’ar motocin tokumbo, kuma ya rayu ne a Gundumar Middleburg Mpumalanga. Kafin rasuwarsa wasu ‘yan Afirka ta Kudu su biyu sun nuna ra’ayin sayen wata motarsa fara kirar VW polo.

“Sun shirya kan wani farashin da suka aminta su biya, kuma Henry ya gabatar da duk takardun da ake bukata don kammala cinikin, a lokacin ne mutanen suka ce suna son su dana motar kafin su biya” In ji Okoli.

Kamar yadda yace, Henry ya yarda da bukatarsu amma yace yana bukatar ya shiga motar su tuka da shi.

“A lokacin da suke tukin motar sai ya fahimci cewa ‘yan fashi ne, kumas uka bukace shi da ya ba su makullin motar. Daga nan sai suka far masa ta hanyar daba masa wuka a jikinsa, a wurare da dama, suka karbi makullin, amma suka kasa tserewa da motar.

Koli ya kara da cewa abunda suka aikata ya jawo hankalin mutanen dake kusa, inda suka samu tserewa da makullin kawai bada motar ba. An garzaya da marigayi Henry zuwa wata assibiti amma ashe rai yayi halinsa.

Yace tuni shugaban kungiyar NICASA na Lardi ya shigar da kara kan aikata fashi da makami da kisan gilla, a kotun Mpumalanga.

“Mai girma Jekadan Najeriya, hare-haren da ake kai ma ‘yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu sunyi muni, kuma muna bukatar yin wani abu cikin gaugawa don magance mummunan aikin. ‘Yan kasar mu na fuskantar hare-hare a kasar Afirka ta Kudu. Ana kai muna hari ta ko’ina.

Yayi kira ga ofishin jekadancin da ya gaggauta yin wani abu kan haka.

“Ba mu da wata sakewa, mun zama tamkar abun farautar kowa. Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu mun gaji da aiko da gawarwakin ‘yan’uwanmu da ake kashewa zuwa gida” In ji Koli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel