Ya kashe Kansa da Mahaifiyarsa Mai Shekaru 57

Ya kashe Kansa da Mahaifiyarsa Mai Shekaru 57

- Wani matashi ya kashe Kansa da Mahaifiyarsa Mai Shekaru 57

- Tuni 'yansanda suka fara gudanar da bincike kan yadda al’amarin ya faru.

Wani mugun abu ya faru a Ekan Ikare Akoko dake jihar Ondo, a lokacin da wani mutum ya kashe mahaifiyarsa mai suna Mrs Ajimo, wadda aka fi sani da Mama Gbenga, kafin ya kashe kansa.

Matar wadda tayi rayurwata a garin Akure, ta mutu ne a lokacin da take artabu da sanannen mai laifin danta da ake kira Ayotunde Gbenga Opeyemi.

An ruwaito cewa matar ta haifi yara ukku da tsohon mijinta a garin Ikare Akoko kafin ta koma Akure inda ta auri wani mijin.

Daya daga cikin yaranta ne Gbenga ya kashe ta kuma ya gudu zuwa Ikare Akoko, inda yake zaune da kakarsa a rukunin gidajen Ekan.

A lokacin da ya fahimci cewa ana kokarin mika shi ga ofishin ‘yansanda naYankin Ikare, sai ya sulale cikin dare zuwa dakin sanwa wurin da ya rataye kansa.

Mazauna unguwar sunce abun ya faru ne a lokacin da duk mutanen gidan ke bacci. Wani daga cikin danginsu da ya fito da misalin karfe ukku na dare don kewayawa ya ga jikin Gbenga na reto kuma yayi ihun da ya jawo hankalin mutane da dama.

Wata majiyar ‘yansada a Akoko da ta tabbatar da faruwar al’amarin tace tuni aka fara gudanar da bincike kan yadda al’amarin ya faru.

KU KARANTA: An damke tsoho da muggan kwayoyi zai tafi Saudiyya

Wata majiyar ‘yansada a Akoko da ta tabbatar da faruwar al’amarin tace tuni aka fara gudanar da bincike kan yadda al’amarin ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel