‘Yan Sanda sun kama Mai gida da Matarsa za su saida Yaron su a Anambra

‘Yan Sanda sun kama Mai gida da Matarsa za su saida Yaron su a Anambra

Wani labari mai ban mamaki ya fara ratsa ko ina a Najeriya bayan da aka ji wasu ma’aurata su na shirin saida yaron da su ke da shi a Duniya.

Jami’an ‘Yan Sanda da ke jihar Anambra, sun yi nasarar damke wannan Iyayen da su ke da niyyar saida yaron su namiji a kan kudi N30, 000.

Kakakin ‘Yan Sanda na jihar, PPRO Haruna Mohammed, ya bayyana cewa sun kama wadannan mutane ne da su ka shirya saida ‘Dan cikin su.

‘Yan Sandan sun yi ram da Magidantan ne a Ranar Talata 30 ga Watan Mayun 2019 da rana tsaka kimanin karfe 2:00 kafin su saida ‘Dan na su.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje za ta aurar da wasu Zaurawa a Jihar Kano

Wani Chinonso Anyanwu mai shekara 32 da kuma Mai dakinsa mai suna Oluebube mai shekaru 20 da haihuwa, su ne su ke da wannan mugun nufi.

Wannan Magidanta sun shirya tsaf ne domin saidawa wata mata mai suna Misis Sandra Odimege da ta fito daga Jihar Imo yaron da su ka haifa.

Odimege da ta so ta sayi wannan yaro, ta fito ne daga wani Kauye da ake kira Umezike da ke Garin Amorka a cikin karamar hukumar Ihiala a Anambra.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel