Kotu ta kwace kadarori 214 daga hannun barayin gwamnati saba'in

Kotu ta kwace kadarori 214 daga hannun barayin gwamnati saba'in

Hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati ta EFCC, ta samu nasarar kwato kadarori 214 cikin garin Abuja, Legas, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kogi, Adamawa, Oyo da kuma wasu jihohi daban-daban a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018.

Hukumar mai fafutikar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa bisa ga umurnin Kotu, ta samu nasarar kwato kadarori da dama daga hannun barayin gwamnatin fiye da saba'in a fadin kasar sakamakon miyagun laifuka masu nasaba da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Cikin binciken da manema labarai na jaridar The Punch su ka gudanar a ranar Juma'ar da ta gabata ya tabbatar da cewa, hukumar ta samu nasarar kwace kadarori daga hannu barayin gwamnati da suka hadar da; Ima Niboro, kakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kotu ta kwace kadarori 214 daga hannun barayin gwamnati saba'in

Kotu ta kwace kadarori 214 daga hannun barayin gwamnati saba'in
Source: Depositphotos

Sauran mashahuran 'yan Najeriya da suka rasa mallakin kadarorin su bisa ga umurnin kotu sun hadar da; tsohuwar Ministan man fetur Diezani Alison Madueke, tsohon shugaban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Sambo Dasuki, tsohon Minista Iyorchia Ayu.

Tsohon shugaban ma'aikatan dakarun tsaro, Marigayi Alex Badeh, tsohon shugaban hafsin dakarun sojin sama, Air Marshal Adesola Amosu, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda, tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema da kuma Kanal Bello Fadile.

Jerin sunayen ya hadar da George Turner, wanda kotu za ta kwace kadarorin sa 17 cikin sassa daban-daban a jihar Bayelsa, tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da kuma Garba Birnin Kudu wanda za a kwace kadarori 14 da suka mallaka.

Kazalika hukumar EFCC ta kwace kadarori uku a garin Abuja mallakin Emmanuel Ozigi da wasu mutane biyu. Hukumar ta kuma samu nasarar a kan wasu kadarori shida cikin sassa daban-daban a jihar Oyo mallakin wani Oni Ademola.

KARANTA KUMA: Gwamnati za ta yiwa Makarantun Almajirai tsarki a jihar Kano

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar EFCC ta kwace kadarori na alfarma da dama a jihohin Legas, Ribas da kuma Abuja mallakin tsohuwar Ministan man fetur a gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan.

Cikin ire-iren kadarori na biliyoyin Naira da kotu ta bayar da umurnin kwace mallakin su daga hannun masu yiwa tattalin arziki ta'annati sun hadar da gidaje, masana'atu, gonaki, asusun ajiya na bankuna daban-daban da makamantan su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel