‘Yan fashi sun kashe mutane 41 a Zamfara cikin mako daya

‘Yan fashi sun kashe mutane 41 a Zamfara cikin mako daya

- ‘Yan fashi sun kashe mutane 41 a Zamfara cikin mako daya

- An bada rahoton cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun kashe a kalla mutane 41 a jihar Zamfara cikin makon da ya gabata.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, an kashe mutane 15 a karamar hukumar mulki ta Bungudu, shidda a Birnin Magaji da kuma 20 a kauyen Kunkulai dake gundumar Magami a karamar hukumar mulkin Gusau.

A halin yanzu kuma, mutane biyar da aka sace ranar Larbar data wuce a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati dake Moriki har yanzu ba a sako su ba. Kuma wa’yanda ke garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.

Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar sojoji Major Clement Abiade ya fada ma majiyarmu cewa a halin yanzu rundunar sojoji na nan ta baza komarta don gano wadanda ake garkuwa da su. Jami’in sojan yace: “Ba mu yi saku-saku da al’amarin ba.”

KU KARANTA: Wata kotu a Abuja ta tsare wasu ‘yan kasuwa sabodashiga haramtacciyar kungiya

Yace, rundunar sintiri ta hadin gwiwar ‘yansanda da sojoji na zurfafa bincike cikin dazuka amma har yanzu ba wani bayani.

Mun aje wata rundunarmu kusa ga makarantar sakandaren don kiyaye afkuwar abunda ya faru a nan gaba.”

A ranar Alhamis, wasu mutane da suka fusata sun kashe Fulani shidda a fadar Sarkin Birnin Magaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel