Shugabancin majalisu: Mambobi da shugabannin PDP sun zabi 'yan takarar da zasu goya wa baya

Shugabancin majalisu: Mambobi da shugabannin PDP sun zabi 'yan takarar da zasu goya wa baya

Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP sun fara tuntubar sabbin mambobin majalisar wakilai da na dattijai da aka zaba a tutar jam'iyyar da kuma wadanda aka zaba a jam'iyyar APC mai mulki domin ganin an gudanar da zaben sabbin shugabannin majalisu cikin lumana.

Shugabannin na PDP, kamar yadda majiyar mu ta sanar da mu, na son ganin mambobin jam'iyyar su a majalisu biyu na tarayya sun jingine duk wata niyya ta nuna hamayya a kan 'yan takarar shugabancin majalisa da jam'iyyar APC ke son a zaba.

Daga cikin wadanda suka bijiro da wannan mataki sun hada da wasu daga cikin sabbin zababbun gwamnoni, gwamnoni masu barin gado da wasu shugabannin jam'iyyar PDP.

"Wadannan shugabanni da jagororin jam'iyya sun bullo da wannan tunani domin canja fuskar PDP daga kallon da ake yi mata na mai yin katsalandan a harkokin bangaren gudanarwa na gwamnati," kamar yadda daya daga cikinsu ya shaida wa majiyar mu.

Bayan shugabanni da jagororin jam'iyyar PDP, rahotannin sun bayyana cewar akwai wasu manyan 'yan Najeriya da ba 'yan siyasa ba dake kokarin ganin an gudanar da zaben shugabannin majalisar cikin salama.

Shugabancin majalisu: Mambobi da shugabannin PDP sun zabi 'yan takarar da zasu goya wa baya

Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Wani daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP ya bayyana cewar; "zan iya tabbatar muku cewar shugabannin majalisa na yanzu da shugabancin jam'iyyar PDP sun sha zama tare da wasu manya a kasar nan domin tattauna yadda za a gudanar da zaben shugabannin majalisa na gaba cikin lumana."

Tuni wasu daga cikin mambobin jam'iyyar PDP a majalisar wakilai suka bayyana goyon bayansu ga takarar Femi Gbajabiamila.

DUBA WANNAN: A karshe: Rundunar soji ta bayyana masu daukan nauyin aiyukan ta'addanci a Najeriya

Mambobin jam'iyyar PDP a majalisar dattijai na cigaba da tattauna wa da Sanata Ahmed Lawan a kan batun rabon mukamai a majalisar dattijai, wanda da zarar sun kammala hakan zasu fito fili su bayyana goyon bayansu ga takarar sa.

Majiyar jam'iyyar PDP ta ce: "mun yi haka ne domin a samu zaman lafiya a majalisa da kuma tabbatar wa 'yan Najeriya cewar jam'iyyar PDP ta canja. Za mu yi haka ne domin samun natsuwar mayar da hankali a kan yadda zamu dawo da farinjinin mu domin mu cigaba da lashe zabe kamar yadda muke yi a baya.

"Wasu daga cikin mu na da ra'ayin cewar ba siyasa ba ce mu yi kokarin hana jam'iyya mai ci dake da rinjaye ta kafa samar da shugabannin majalisa. Hakan ba yana nufin mu na son a samu shugabannin jam'iyya da zasu zama rakumi da akala a hannun bangaren zartar wa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel