Segun Oni: Dattawan APC a Ekiti ba su yarda da matakin Jam’iyya ba

Segun Oni: Dattawan APC a Ekiti ba su yarda da matakin Jam’iyya ba

Mun samu labari cewa ana samun rabuwar kai a tsakanin manyan ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ekiti. Hakan na zuwa ne bayan da jam’iyyar ta dauki matakin dakatar da shugaban ta a Kudu, Segun Oni.

Wasu Dattawa na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ekiti, sun fito sun nuna cewa ba su yarda da dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na reshen kudancin Najeriya, Segun Oni da aka yi ba. Jiga-jigan na APC sun ce babu hannunsu.

Michael Durodola, Tayo Okanlawon, Ebenezer Ogunlana da kuma Sola Ilori, su ne su kayi magana a madadin Dattawan jam’iyyar APC na yankin Ifaki da Ido/Osi, inda su kace an sabawa tsarin mulki wajen dakatar da Cif Segeun Oni.

A jawabin wadannan Dattawa na APC da su ka rattabawa hannu a madadin sauran shugabannin jam’iyyar na fadin jihar Ekiti, korar Segun Oni daga ofis na wani ‘dan lokaci da aka yi, abin kunya ne kuma wanda sam bai dace ba.

KU KARANTA: Dattijon Arewa ya fadi inda ya kamata mulki ya koma a 2019

Segun Oni: Dattawan APC a Ekiti ba su yarda da matakin Jam’iyya ba
Jam’iyyar APC ta shiga rikici bayan an dakatar da Oni
Asali: Facebook

Ana zargin Segun Oni da yi wa jam’iyyar APC mai mulki zagon-kasa ta hanyar hada-kai da ‘Yan adawa. Wadannan Dattawa sun ce laifin da ake zargin tsohon gwamnan da shi ba gaskiya bane, kuma ba ayi bincike yadda ya kamata ba.

Wadannan jagorori na APC har wa yau, sun ce ba a gayyaci Segun Oni domin ya wanke kan-sa ba, kuma babu sa hannun ‘yan kwamitin da su kayi wannan aiki, sai dai kurum aka ji cewa APC ta dakatar da Segun Oni a Mazabarsa.

Shugaban APC na yankin Ifaki, Shina Akinloye, da Sakataren jam’iyyar, Ogunyemi Taiwo, da kuma sauran shugabannin jam’iyyar mai mulki 24 da ke karamar hukumar Ifaki ne su ka sa hannu a takardar dakatar da Oni kwanakin baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel