A karshe: Rundunar soji ta bayyana masu daukan nauyin aiyukan ta'addanci a Najeriya

A karshe: Rundunar soji ta bayyana masu daukan nauyin aiyukan ta'addanci a Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya tayi zargin cewar wasu kungiyoyin kasashen ketare dake aiki tare da wasu kungiyoyin ta'addanci na cikin gida Najeriya ne ke daukan nauyin aiyukan ta'addanci a cikin kasar nan.

A cewar rundunar sojin, masu daukan nauyin aikata laifukan na kokarin ganin sun hana duk wani yunkurin dakile aiyukan ta'addanci a cikin gida Najeriya da Afrika tasiri.

Rundunar ta kara da cewa kungiyoyin basu tsaya a iya kan wannan muguwar akida tasu ba, ta bayyana cewar yanzu haka suna shirya makarkashiyar yadda zasu kawo wa dimokradiyyar kasar nan nakasu da kuma kawo cikas a ranar rantsuwar sabbin shugabannin da aka zaba, wanda za a yi ranar 29 ga watan Mayu.

A wani jawabi da ta fitar a ranar Asabar ta bakin darektan yada labarai da hulda da jama'a, Kanal Sagir Musa, rundunar sojin ta ce; "masu daukan nauyin aiyukan ta'addancin na son zubar da mutuncin Najeriya ta hanyar ganin sun hana kasar zaman lafiya."

A karshe: Rundunar soji ta bayyana masu daukan nauyin aiyukan ta'addanci a Najeriya

Sojojin Najeriya
Source: Twitter

"Mun san cewar akwai wasu marasa kishi a cikin Najeriya da suka hada kai da wasu kungiyoyin kasashen ketare domin hana Najeriya da yammacin Afrika zama lafiya.

"Akwai wadanda daga kalamansu ka san suna goyon bayan 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci. Alal misali, mu na da sahihan bayanai cewar akwai wasu daga cikin irin wadannan marasa kishin kasa da ke tattauna wa da kungiyar Boko Haram domin su basu tallafi, yayin da wasu daga cikin su ke kirkira tare da yada karya a kan rundnar soji domin sanyaya musu gwuiwa a yakin da suke yi da ta'addanci da 'yan ta'adda," a cewar jawabin.

DUBA WANNAN: Wuya: Halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga bayan sojoji sun tagayyara su

Jawabin ya kara da cewa wadannan mutane da kungiyoyi sun hada kai domin ganin sun samar da kudi da kayan aiki ga kungiyar ta'addanci ta ISWAP (reshen kungiyar IS da ke yankin Afrika ta yamma) da 'yan bindiga domin su cigaba da kai hare-hare a kan jama'a.

Rundunar sojin ta kara da cewa bayan duk wannan abu da masu daukan nauyin aikin ta'addanci ke yi, su na cigaba da kulla yadda za su haifar da rashin jituwa a tsakanin dakarun rundunar sojin hadin gwuiwa na kasashen gefen tekun Chadi (MNJTF) da kulla yadda za su kawo cikas a ranar da za a rantsar da sabbin zababbun shugabanni, ranar 29 ga watan Mayu.

Rundunar sojin ta ce babu abinda zai sanyaya mata gwuiwa wajen ganin ta cigaba da yakar duk wani aikin ta'addanci da 'yan ta'adda da kowanne irin suna suke amfani, kuma ko waye ke daukan nauyin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel