‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Sojoji hari a cikin Garin Magumeri

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Sojoji hari a cikin Garin Magumeri

Mun samu labari cewa Mayakan Boko Haram sun yi nasarar karbe wani yanki da Sojojin Najeriya ke da iko a kai. Mazauna wannan yanki da kuma jami’an tsaro su ka tabbatar mana da wannan labari.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan an kai wani hari da ya bar gawar Sojojin Najeriya 5, sannan kuma aka nemi wasu Sojojin aka rasa. Wannan hari ya nuna cewa har yanzu ana fama da rikicin ‘yan ta’ddan.

A jiya Asabar 4 ga Watan Mayu, mu ka ji cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Rundunar Sojojin kasar nan da ke Garin Magumeri a jihar Borno hari. Tsawon tafiyar kilomita 50 ne tsakanin Magumeri zuwa cikin Maiduguri.

KU KARANTA: Abin da ya sa har gobe ake satar mutane a Najeriya

Kamar yadda rahoton ya zo mana, ‘Yan ta’addan sun kai hari ne a Ranar Juma’ar nan inda su ka fatattaki Sojojin Najeriya daga sansaninsu. An yi ta faman ba-ta-kashi ne tsakanin Sojojin da ‘Yan ta’addan na wani tsawon lokaci.

Wani jami’in Sojan kasar ya bayyanawa ‘Yan jaridan kasar waje cewa Mayakan Boko Haram sun fatattaki Dakarun Najeriya. Majiyar ta bayyana cewa Sojojin Boko Haram sun karbe makaman Dakarun kasar a wannan farmaki.

KU KARANTA: An rufe Makarantun Boko fiye da 100 a Jihar Filato

Wani rahoto ya tabbatar da cewa an rasa sojojin Najeriya 15 har da wani Laftana a wannan hari, kuma wasu 19 sun samu rauni. Yanzu haka ana kula da masu raunin a Maiduguri. Sauran Sojoji 24 na Bataliyar kuma sun sha da kyar.

‘Yan ta’addan sun iso Garin ne da kimanin karfe 5:00 na yamma. Bayan wuta yayi wuta, Sojojin Najeriya sun tsere zuwa cikin daji bayan an ci karfinsu. Daga baya ne dai aka kawowa Dakarun dauki daga cikin Garin Gubio da ke jihar.

Mayakan na Boko Haram da su ka addabi yankin Arewa maso gabas sun zauna cikin sansanin Sojojin kasar na kimanin sa’a 4 kafin wasu Dakaru su zo su fatattakesu daga yankin cikin dare inji jaridar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel