Buhari ya daukewa na-hannun daman sa da Jagororin APC kafa wajen nada Ministoci

Buhari ya daukewa na-hannun daman sa da Jagororin APC kafa wajen nada Ministoci

Labari yana zuwa mana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya zabi ya zakulo Ministocin da zai yi aiki da su ba tare da wani ya sa masa baki ba. Jaridar The Nation ta kasar nan ce ta rahoto mana wannan.

Jaridar take cewa wasu daga cikin manyan na kusa da shugaban kasa Buhari, wadanda har ake tunani su ne ke juya Najeriya a mulkinsa, sun tafi har zuwa Birnin Landan amma kuma aka hana su ganawa da shugaban kasar.

Shugaban kasar ya ki ganawa da wadannan manyan na-kusa da shi da su ka tafi Landan, inda aka sanar da su cewa umarnin da ya bada kenan. Yanzu haka dai babu wanda ya san shiga-da-ficen shugaban kasar sai shi kurum.

Wadanda su ka tafi Landan da nufin ganin shugaba Buhari watakila domin sa baki a nadin sababbin Ministoci ba su iya ganawa da shugaban kasar ba. Majiyar tace wani Minista ne kurum aka ba dama ya ga shugaban kasar.

KU KARANTA: Wani Sanata daga Jihar Shugaban kasa yayi sa-in-sa da Shehu Sani

Buhari ya daukewa na-hannun daman sa da Jagororin APC kafa wajen nada Ministoci

Shugaban kasa ya ki kula manyan APC a wajen nada sababbin Ministoci
Source: Facebook

Labarin da mu ka ji shi ne har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wannan Minista da ya samu damar ganin shugaban kasar yana tare da shi a Landan. Majiyar ba ta bayyana mana ko wane daga cikin Ministocin kasar bane wannan.

Shugaban kasar dai ya canza ne daga halin da aka san sa kwatsam a rana daya. Ana tunani wannan bai wuce saboda shirin da yake yi na zakulo kwararru su rike masa ofishin Ministoci a gwamnatinsa a wa’adinsa na wannan karo.

Yayin da ake jin cewa babu wanda ya san wadanda ake shirin ba kujerar Minista, wani daga cikin gwamnonin APC ya bayyana cewa shugaban kasar bai nemi gwamnoni su kawo masa jerin wadanda su ke so a Ministoci daga jihohin su ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel