Ta faru ta kare: Hukumar soji ta bayyana wadanda ke da hannu a matsalar tsaron Najeriya

Ta faru ta kare: Hukumar soji ta bayyana wadanda ke da hannu a matsalar tsaron Najeriya

- Hukumar sojin Najeriya ta bayyana mutanen da suke so su ta da zaune a kasar nan ranar da za a rantsar da zababbun 'yan siyasa a kasar nan

- Hukumar ta ce mutanen suna hada baki da 'yan Boko Haram da kuma sauran 'yan ta'adda a kasar nan domin su cigaba da tada rikici a fadin kasar nan

A yau Asabar dinnan ne hukumar soji ta kasa, ta yi zargin cewa da akwai wasu mutane da suke hada kai da wasu 'yan kasashen waje domin kawo tsaiko a ranar rantsar da zababbun gwamnonin kasar nan wanda za ayi ranar 29 ga watan Mayu.

"Mutanen da su ke shirin kawo rikicin a kasar nan sunyi tunanin cewa ba za a gabatar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba, sai ga shi mun basu kunya, yanzu su na so su hana gabatar da rantsar da zababbun 'yan siyasar kasar nan," in ji kakakin hukumar soji, Col. Sagir Musa.

Ta faru ta kare: Hukumar soji ta bayyana wadanda ke da hannu a matsalar tsaron Najeriya

Ta faru ta kare: Hukumar soji ta bayyana wadanda ke da hannu a matsalar tsaron Najeriya
Source: Twitter

Musa ya yi zargin cewar mutanen suna so su yi amfani da wannan damar ne wurin tada rikici a fadin kasar nan, dama yankin nahiyar Afrika ta kudu baki daya.

Sannan ya kara zargin cewa mutanen suna so su biyo wata hanya ta yin amfani da 'yan ta'addar Boko Haram, da kuma 'yan bindiga da ke kasar nan wurin ba su kudi da makamai domin su ta da rikici a kasar nan.

KU KARANTA: Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

"Misali, alamu sun nu na cewa wasu mutane suna hada baki da 'yan kungiyar Boko Haram, sannan wasu kuma suna yada labaran karya a cikin al'umma, domin su hada al'ummar kasa da hukumar soji fada," in ji Musa.

Ya gargade su akan su dai na abinda su ke yi idan ba haka ba kuma hukumar za ta dau kwakkwaran mataki akan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel