Malami ya tsiyayarwa da dalibin ruwan ido, saboda tsananin duka da bulala

Malami ya tsiyayarwa da dalibin ruwan ido, saboda tsananin duka da bulala

- Wani malamin makarantar sakandare ya tsiyayar da idondalibin shi, saboda tsananin duka da bulala

- Shugaban makarantar ya ce tabbas malamin ya yi laifi tunda dama ba a duka a makarantar su

Wani tsautsayi da ya afka kan wani dalibin makarantar sakandare ta David Camp Academy da ke Ogba, jihar Lagos, ranar Juma'a 29 ga watan Maris ta zamto rana wacce Daniel Agboola ba zai ta ba mancewa da ita ba. Ita ce ranar da malamin shi Mr. Oludare Olaleye, ya fasa mishi kwayar idon shi na bangaren dama a lokacin da ya ke dukan shi da bulala.

Dalibin da malamin sun samu sabani, inda malamin ya ke zargin Daniel da cewa ya taka shi lokacin da ya ke shirin fita daga aji.

Malami ya tsiyayarwa da dalibin ruwan ido, saboda tsananin duka da bulala

Malami ya tsiyayarwa da dalibin ruwan ido, saboda tsananin duka da bulala
Source: Facebook

Sanadiyyar hakan ne ya sa malamin ya dauki bulala ya dinga dukan shi da ita har ta kubce ta sami kwayar idon sa na bangaren dama.

A bayanin da shugaban makarantar ya yi wa manema labarai, ya bayyana cewa:

"Matsala ce aka samu tsakanin malami da dalibi, inda malamin ya yi kokarin dukan dalibin, tsautsayi ya sa dalibin ya cire hannun shi daga kan idonshi, sai bulalar ta sami kwayar idon shi na bangaren dama. Hakan shi ne ainahin abinda ya faru.

KU KARANTA: Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

"Laifin malamin ne tabbas, saboda ba ma bari ana dukan daliban mu da bulala a makarantar nan. Muna da doka a nan, saboda muna da jami'ai guda biyu wadanda idan yaro ya yi laifi suke yi masa hukunci. Saboda haka malamin ba shi da wani iko da zai iya daga bulala ya daki dalibin tun a farko.

"Bayan haka kuma, ina son sanar da ku cewa babu wata matsala da idon yaron ya samu, a sakamakon da asibiti suka bamu ya nuna cewa idon shi kalau ya ke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel