Tashin hankali: Yan bindiga sun kaiwa Bafarawa mumunan harin har gidansa

Tashin hankali: Yan bindiga sun kaiwa Bafarawa mumunan harin har gidansa

Yan bindiga sun kai mumunan hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa inda suka kashe mutum guda, kuma sukayi garkuwa dan danuwansa awa 12 bayan yayi raddi kan yan ta'adda

Wannan harin yazo ne a kalla sa'o'i 24 bayan tsohon gwanman ya kaddamar da gidauniyarshi a Abuja wacce yake niyyar amfani da ita domin taimakawa wajen magance matsalolin taaddanci da garkuwa da mutane musamman a arewacin Najeria.

Yan ta'addan kuma sunyi garkuwa da dan danuwanshi mai kimanin shekaru 16 mai suna Abdurrasheed Saidu wanda yake a gidan a lokacin.

KU KARANTA: Wasu ma’aikatan kamfanin lantarki sun shiga hannun hukuma

Yayinda yake tabbatar da harin da aka kai, babban jamiin gidauniyar Dr. Sulaiman Shuaibu Shinkafi yace an kai harin da misalin karfe 9 na marece a ranar jumaa.

Shinkafi ya kara da cewa maharan, wanda sunkai kimanin mutum 60 dauke da bindiga kirar Ak 47 sunzo ne akan babura kuma sun sayi mai na naira 5000 a garin kafin kai harin a gidan.

Da aka tuntubi mai magana da yawun yansanda na jihar Sokoto DSP muhammad Sadiq yace bashi da masaniya game da wannan harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel