Ramadan: Sarkin musulmi ya umarci ‘yan Najeriya

Ramadan: Sarkin musulmi ya umarci ‘yan Najeriya

-Za'a fara duban watan Ramadana ranar Lahadi 5 ga watan Mayu, 2019

-Ranar Lahadi 5 ga watan Mayu zai kasance 29 ga watan Sha'aban 1440 bayan hijira

Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar yayi kira ga al’ummar musulmin Najeriya da su dubi jinjirin watan Ramadan.

Sarkin yayi wannan kiran ne a wani zance da ya fito daga wurin Farfesa Sambo Junaidu wanda shine shugaban kwamtin duban wata na majalisar Sarkin.

Ramadan: Sakin musulmi ya umarci ‘yan Najeriya

Ramadan: Sakin musulmi ya umarci ‘yan Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA:Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu

Junaidu yace, “ wannan sanarwa dai ta kasance tunatarwa ce da cewa ranar Lahadi 5 ga watan Mayu shine yayi daidai da 29 ga watan Sha’aban na shekarar 1440 bayan hijira, a don haka yayi daidai da ranar da za’a dubi watan Ramadan.

“ A dalilin haka ake bukatar al’ummar musulmi da su fito neman watan Ramdana a yammacin Lahadi idan har Allah yasa sun gani suyi gaggawar sanar da mai unguwa ko kuma hakima mafi kusa dasu wanda daga nan zai tutunbi fadar Sarkin musulmi.”

Sarkin ya roki Allah da ya tsare jagororin musulmai da kuma musulmi baki daya a lokacin da suke gudanar da al’amuran da suka shafi ibada.

Bugu da kari, ya bayyana lambobin wayar da za’a iya tuntuba idan har aka samu labarin ganin watan na Ramadana domin sanar da fadarsa kamar haka:

08037157100, 07067416900,

08066303077, 08065480405,

08035965322, 08036149757 da kuma

08035945903.

Ramadan shine wata na 9 cikin jerin watannin musulunci wanada aka wajabta yin azumi a cikinsa tsawon wata guda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel