Gwamnatin Jihar Plateau Ta Rufe Sama Da Makarantu 100 Da Aka Buda Ba Kan Ka’ida

Gwamnatin Jihar Plateau Ta Rufe Sama Da Makarantu 100 Da Aka Buda Ba Kan Ka’ida

- Gwamnatin Jihar Plateau Ta Rufe Sama Da Makarantu 100 Da Aka Buda Ba Kan Ka’ida Ba

- Wasu daga cikin makarantun ba a ba su damar gudanar da iki ba

Gwamnatin jihar Plateau ta rufe sama da makarantu 100 da aka buda ba kan ka’ida ba a cikin kananan hukumomin mulki 17 dake jihar, Kwamishinan ilimin makarantun sakandare na jihar, Mr Jude ne ya bayyana hakan.

Dakur ya fadi hakan ne a garin Jos, ranar Jumu’a, a lokacin da yake karbar wata kyauta kan darajar dan Adam da ilmi wadda wata kungiyar bincike ta ba shi.

Kwamishinan yace makarantun da aka rufe a cikin shekarar 2018 ba su cika ka’idar zama makarantun koyar da yara ba, wadanda sune shugabannin wannan kasar a nan gaba.

KU KARANTA: https://hausa.legit.ng/1236696-wani-likita-ya-makala-wa-yara-65-da-manya-25-cutar-kanjamau

“Wasu daga cikin makarantun ba a ba su damar gudanar da aiki ba, wasu kuma ba su da kwararrin malamai da kyakkyawan muhallin koyarwa” in ji kwamishinan.

Dakur yace gwamnati nada kudurin inganta ilimi a jihar ta hanyar tsaurarawa wurin ganin an bi ka’idar gudanarwa ingantatta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel