JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan siyasa da su kayi magudin jarabawa

JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan siyasa da su kayi magudin jarabawa

Ishaq Oloyole, Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, (JAMB) ya ce hukumar ta gano wasu manyan 'yan siyasan Najeriya da suka dauki sojojin gona suka rubuta musu jarabawar.

Shugaban na JAMB ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a yayin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na Cibiyar Ilimi ta Najeriya.

Ya ce sakamakon binciken da su kayi na magudin zabe tsakanin shekarar 2009 zuwa 2019 zai bawa 'yan Najeriya mamaki sosai.

JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan Najeriya da su kayi magudin jarabawa

JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan Najeriya da su kayi magudin jarabawa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina

Oloyele ya ce duk da cewa hukumar ba za ta iya hukunta wadanda aka samu da laifin ba tunda sun karbi sakamakon su tuni sunyi gaba, za a wallafa sunayensu domin a kunyata su.

Ya ce kuma hukumar ta dauki hayar babban lauya mai makamin SAN da zai gurfanar da mutane 100 da aka kama da laifin aikata magudin zabe yayin jarabawar UTME da aka gudanar tsakanin ranar 11 zuwa 18 ga watan Afrilu a sassan kasar nan daban-daban.

Shugaban na JAMB bai bayyana sunan babban lauyan da hukumar ta dauka ba domin gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin magudin zaben.

Bai kuma bayyana ranar da za a fitar da sakamakon jarabawar UTME na bana ba.

"Na dauki hayar babban lauya mai mukamin SAN wanda tsohon mai shari'a ne a kasar nan domin ya taimaka wurin ganin dukkan wadanda aka samu da laifi sun fuskanci hukunci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel