Wata Kotu a Abuja ta tsare wasu ‘yan kasuwa 2 saboda shiga haramtacciyar kungiya

Wata Kotu a Abuja ta tsare wasu ‘yan kasuwa 2 saboda shiga haramtacciyar kungiya

- Kotu ta tsare wasu ‘yan kasuwa 2 saboda shiga haramtacciyar kungiya

- ‘Yansanda sun caji Mathew Bamiro mai shekaru 26 da Jacob Panshak dan shekaru 34 wadanda ke zaune a garin Lugbe dake Abuja da laifin kwace

Wata babbar kotun yanki dake Mpape Abuja a ranar Alhamis ta bada umurnin a tsare wasu ‘yan kasuwa biyu a kurkuku, saboda zargin da ake masu na shiga wata haramtacciyar kungiya.

‘Yansanda sun caji Mathew Bamiro mai shekaru 26 da Jacob Panshak dan shekaru 34 wadanda ke zaune a garin Lugbe dake Abuja da laifin kwace, da kuma shiga wata haramtacciyar kungiya mai suna “Arobaga”

Mai shari’a Hassan Mohammed ya bada umurnin bayan Bamiro da Panshak sun karba aikata laifin da ake zargin su da shi, tare da rokon kotu ta tausaya masu.

Alkali Mohammed ya daga shari’ar zuwa 8 ga watan Mayu 2019, don samun cikakkar shaida da yanke hukunci.

KU KARANTA: https://hausa.legit.ng/1236696-wani-likita-ya-makala-wa-yara-65-da-manya-25-cutar-kanjamau.html

Mai shigar da kara Edwin Ochayi, ya fada ma kotu cewa a ranar 17 ga watan Maris, Sajen Collins Igwu da Oyama Paul sun kai rahoton al’amarin a ofishin yanki na ‘yansanda dake Lugbe. Ochayi yace a ranar 16 ga watan Maris wa’yanda ake kara tare da wasu ‘yan kungiyar ta Arobaga (wadanda suka gudu) sun kai hari ga ‘yan kungiyar da suke hamayya da ita da miyagun makamai, kuma sun sace wata wayar salula kirar Infinix da wayoyi kirar Tecno ukku daga hannun mutanen da suka kai ma harin, a dakin saida barasa na Corban dake Lugbe.

Mai shigar da karar yace an tura masu laifin daga ofishin ‘yansanda na Trade More zuwa Sashen Binciken Laifuffuka dake Abuja.

Yace daga baya kuma aka tura su zuwa ofishin rundunar ‘yansandan yaki da fashi da makami wurin da wadanda ake zargin suka karba laifinsu. Ochayi yace aikata laifin ya saba ma Sassan Kundin Shari’a na 97, da 292 da kuma 973.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel