Ban taba tunanin zanyi siyasa ba, inji sanata Lawan

Ban taba tunanin zanyi siyasa ba, inji sanata Lawan

-Demokradiya akeyi saboda haka kowa yanada 'yancin tsayawa takara, inji sanata Lawan Ahmad

-Sanata Lawan Ahmad ya fadi lokacin da ya fara siyasa a wata tattaunawa da yayi da yan jarida

Sanata Lawan Ahmad wanda shine shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa kuma dan takarar zama shugaban majalisar dattawa ta 9 a wata tattaunawa da akayi dashi ya fadi abinda yake da niyyar yi idan aka zabe shi, ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:

Ya kake gudunar da kamfe dinka kasancewar daga cikin abokan karawar taka akwai yan jam’iyarka ciki?

Ban taba tunanin zanyi siyasa ba, inji sanata Lawan

Ban taba tunanin zanyi siyasa ba, inji sanata Lawan
Source: Depositphotos

KU KARANTA:An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna

Lawan: Wannan shi ake kira demokradiya. Duk wanda ke ganin yanada gudumuwar da zai iya badawa sai ya fito takara. Ni ba bakon takara bane, wannan karo shine wa’adina na 6 a majalisar dokoki ta kasa saboda tun shekarar 1999 nake majalisar. Ko kafin wannan ma na taba yin takara a baya karkashin UNPC.

Me zaka iya cewa akan siyarsarka, daga lokacin da ka fara zuwa yanzu ka cinma wani mataki na cigaba kuwa ko ya abin yake?

Lawan: Na fara siyasane a shekarar 1998 a mastayin mataimakin shugaban jam’iyar APP na jihar Yobe. Daga bisani kuma na tsaya takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar Bade/Jakusko kuma na samu nasara a shekarar 1999. Daga nan ne tarihin siyasata ya fara har zuwa matsayin da nake kai a yanzu, zan iya cewa na samu cigaba kwarai da gaske.

Ya akayi kayi jifa da hular injiniyoyinka ka dauki ta siyasa ka sanyawa kanka?

Lawan: Ba jifa da ita nayi ba. Ban taba tunanin zanyi siyasa ba a rayuwata duka da cewa ina bibiyar jam’iyun dake cigaba a wancan lokaci. Kafin na kasance na fara siyasar jam’iya ina goyon bayan jam’iyar Labour Party ne a zaben shekarar 1992. Karo na farko da na tsaya takara na samu kalubale daban-daban amma Alhamdulillah yanzu muna cikin siyasa kuma komai lafiya lau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel