MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami

MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami

Babban kamfanin sadarwa MTN ta sanar a jiya a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu cewa ta yiwa Sarkin Kano, Mallam Sanusi Lamido nadi a matsayin direkta na musamman a cikin kwamitin direktocin ta.

Nadin da aka yiwa tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN na daga cikin muhimman sauye-sauye da MTN tayi a kwamitin direktocin ta ciki har da nadin Mcebisi Jonas a matsayin Ciyaman.

Mcebisi Jonas tsohon mataimakin Ministan Kudi na a gwamnatin Afirka Ta Kudu wanda ya yi aiki daga 2014 zuwa 2016.

Kamfanin ta kuma kafa wata kwamitin masu bayar da shawarar na kasa da kasa.

MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami

MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Ta ce: "Kwamitin Direktocin na MTN suna ganin kamfanin da shiga sabon shafi a aikace-aikacen ta bayan kallubalen da ta fuskanta sakamakon wasu sauya-sauya da suka faru a baya bayan nan.

"Ana sa ran ciyaman din kwamitin direktoci, Phuthuma Nhleko zai sauka daga mukaminsa a wurin taron da za a gudanar a ranar 23 ga watan Mayun 2019 sannan zai jagoranci mika mulki da kafa sabuwar kwamiti na masu bayar da shawara na kasa da kasa.

"Mcebisi Jonas da aka nada a matsayin Ciyaman zai fara aiki ne a ranar 15 ga watan Disamban 2019.

Baya ga haka muna farin cikin maraba da Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi da Vincent Rague da za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Yulin 2019.

"Mai martaba, Sanusi Lamido Sanusi dan Najeriya ne, Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN. Vincent Rague dan kasar Kenya ne wanda ya yi aiki a fanin kudi na kasa da kasa na tsawon shekaru 24 inda ya rike manyan mukammai da dama.

"Muna fatan sabbin direktocin za su kawo kwarewarsu da basirarsu na aiki ga kwamitin direktocin."

Mallam Sanusi Lamido sarki na 14 a jerin sarakunan Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel