Wani likita ya makala wa yara 65, da manya 25 cutar kanjamau

Wani likita ya makala wa yara 65, da manya 25 cutar kanjamau

- Manya 90, yara kanana 65 likitan ya makala cutar kanjamau

- Ana ganin kasar Pakistan a matsayin kasar dake da karancin yaduwar cutar kanjamau

A kalla mutane 90, da suka hada da kananan yara 65, anka tabbatar da wani likitan dake dauke da cutar kanjamau ya makala masu cutar, a kasar Pakistan, ta hanyar yin amfani da sirinjin allurar da ya gurbata, kamar yadda jami’ai suka ce a ranar Jumu’a.

“Mun kama wani likita bayan mun karbi korafe-korafe daga hukumomin lafiya” In ji Kamran Nawaz, wani jami’in ‘yansandan dake jagorancin sharia’r a kudancin birnin Larkana.

Jami’in ‘yansandan yace: “An fada muna cewa likitan na dauke da cutar kanjamau”

An fara fadakar da hukumomi gameda al’amarin a makon da ya gabata bayan da aka samu yara 18 dauke da cutar kanjamau sakamakon jaraba su da aka yi, wanda ya karfafa ma jami’an lafiya da su gudanar da cikakken bincike.

An gano karin masu dauke da cutar da yawa.

“Sama da mutane 90 aka samu dauke da cutar, kuma yawan kananan yara ya kai 65,” Kamar yadda wani jami’in lafiyar gunduma mai suna Dr. Abdul Rehaman, ya fada ma kamfanin dillancin labaran AFP.

Wani jami’i ya tabbatar da wannan annobar, kodayake ya bada bayani daban kan yawan mutanen da abun ya shafa.

Hukumomi sunce sun bi diddigin abunda ya faru inda suka samu wani likitan da hannnu dumu-dumu, wanda yake amfani da gurbataccen sirinjin allura kan maras lafiya.

Azra Pechuho, Ministan lafiyar yankin ya tabbatar da kama likitan.

KU KARANTA: https://hausa.legit.ng/1236611-mutane-540-suka-rasa-ransu-3-383-suka-jikkata-a-hadurran-watan-janairu-in-ji-hukumar-kiyaye-hadurra-ta-kasa-frsc.html

“Kuma an jarraba jinin iyayen yaran da abun ya shafa, amma ba a same su da cutar ba” In ji Pechuho.

Tuni jami’ai suka dukufa wurin gagarumin shirin binciken jini da ilmantar da mutane.

Ana ganin kasar Pakistan a matsayin kasar dake da karancin yaduwar cutar kanjamau, amma cutar na fadada — mafiyawanci a tsakanin masu amfani da alluran da ake yi a jijiyoyi, karuwai da leburorin da suka tafi aikin kwadago a yankin Gulf.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel