Za'a hukunta 'yan sandan da ake zargin sun yiwa 'yan mata fyade a Abuja

Za'a hukunta 'yan sandan da ake zargin sun yiwa 'yan mata fyade a Abuja

- Rundunar 'yan sandan birnin Abuja ta yi alkawarin hukunta duk wani jami'inta da ta samu da laifin yiwa 'yan matan da suka kamo daga wurin casu a Abuja da daddare fyade

- Hukumar ta ce yanzu haka ta na jiran wasu mutane ne da ta gayyata wadanda za su bayar da shaida akan ainahin abinda ya faru

Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi alkawarin hukunta duk wani dan sanda da ta samu da laifi akan zargin da 'yan matan da aka kamo a gidan casu suke na cewa wasu daga cikin 'yan sandan sun ci zarafin su kuma sun yi musu fyade.

Rundunar ta ce a wata sanarwa da ta fitar ta bakin jami'inta ASP Danjuma Tanimu, ta ce ta sanya kwamiti domin yin bincike akan jami'an 'yan sandan da ake zargin.

Za'a hukunta 'yan sandan da ake zargin sun yiwa 'yan mata fyade a Abuja

Za'a hukunta 'yan sandan da ake zargin sun yiwa 'yan mata fyade a Abuja
Source: Instagram

Ya bayyanawa al'umma cewa hukumar za ta dauki mataki kwakkwara akan duk wanda ta kama da laifi a zargin da 'yan matan su ke na yi musu fyade.

Tanimu ya ce yanzu haka har an fara gabatar da bincike akan jami'an 'yan sandan da ake zargi da laifin aikata fyaden.

KU KARANTA: Wata 'yar Najeriya ta yi kokarin harbe wani dan sanda da ya kamata da kwaya a kasar Italy

Ya ce sun aika da katin gayyata ga wasu mutane da ake tunanin zasu taimaka wurin sanin gaskiyar lamarin.

Bidiyon kamen da jami'an 'yan sandan suka yi ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda ya ke nuni da irin cin zarafi da bugu da jami'an 'yan sandan suka dinga yi wa 'yan matan a lokacin da suka je kama su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel