Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

- An samu asarar rayuka masu yawan gaske sanadiyyar wani mummunan hadari da ya faru a jihar Kano

- Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar hadarin

Kimanin mutane 16 ne ake tunanin sun rasa ransu jiya Juma'a da dare, a wani hadarin mota da ya afku tsakanin wasu motoci guda uku, a kauyen Tukwi da ke kan hanyar Dambatta zuwa Daura da ke jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa, motocin da lamarin ya afku da su suna kan hanyar su ta zuwa karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina, yayin da hatsarin ya afku.

Wani Hakimi a garin Dambatta, Muhammad Jamil Dambatta ya shaidawa manema labarai afkuwar lamarin.

Ya ce mutane 17 ne hatsarin ya shafa, a ciki akwai maza 14 da mata guda uku.

Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano
Source: Depositphotos

Ya ce mutane 14 sun mutu a take a gurin, inda sauran mutane biyu daga cikin ukun da suka rage suka mutu a lokacin da suke karbar magani a asibiti.

Ya bayyana cewa gudun ganganci ne ya jawo hatsarin, inda ya kara da cewa hukumomin tsaro, ciki hadda jami'an hukumar kiyaye hadura sun garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Dambatta.

An yi kokarin a tuntubi jami'an hukumar kiyaye hadura domin samun karin bayani amma hakan bai samu ba.

KU KARANTA: Wata babbar mota ta fadi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama

Bayan haka kuma hukumar 'yan sandan jihar Kano sun samu nasarar kama wani mai Keke Napep mai suna Abu Hussain, mai shekaru 19, da ke zaune a unguwar Maidile, da ke Kano, da laifin kashe wani abokin aikinsa dan shekaru 25 mai suna Mansur Ibrahim.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2 na rana jiya Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel