Buhari zai karbi bakuncin shugaban kwamitin wakilan UN

Buhari zai karbi bakuncin shugaban kwamitin wakilan UN

An sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin Shugaban kwamitin wakilai na Majalisar Dinkin Duniya, Ms Maria Espinosa wadda za ta kawo ziyarar aiki na kwana guda a ranar Litinin a Najeriya.

Mai magana da yawun Espinosa, Ms Monica Gravley ne ta sanar da hakan ranar Juma'a a wurin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatan majalisar da ke birnin New York a Amurka.

A cewarta, ziyarar ta Espinosa na kwana guda zuwa Najeriya yana daga cikin ziyarar aiki na kwanaki takwas da za ta kawo kasashen nahiyar Afirka ta tsakiya da Afirka ta Yamma daga ranar Juma'a.

Buhari zai karbi bakuncin tawagar Majalisar Dinkin Duniya

Buhari zai karbi bakuncin tawagar Majalisar Dinkin Duniya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Kakakin na Espinosa ba ta bayyana abinda shugaban na UN za ta tattauna da Shugaba Buhari ba yayin ganarwarsu a yayin da ta ke amsa tambaya daga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN).

Sai dai ta ce za ta bawa manema labarai bayyanai kai tsaye a lokacin da ake gudanar da taron.

Gravley ta ce wasu 'yan fadar shugaba Muhammadu Buhari za su hallarci ganawar da Espinosa kuma daga baya za su gana da daliban jami'an Abuja.

Ana sa ran Espinosa za tayi jawabi a kan hadin kai tsakanin kasashen duniya da kuma yadda za a magance kallubalen da kasashen ke fuskanta sakamakon sauye-sauye da ake samu inji kakakin na ta.

Shugaban na UN za ta kuma ziyarci kasashen Ghanda da Chadi inda za ta gana da shugabanin kasashen da kuma manyan jami'an gwamantocin kasashen.

Gravely ta kara da cewa "A yayin ziyar ta a nahiyar Afirka, za tayi hira da kafafen yada labarai na cikin gida da na kasa da kasa kuma za ta kira taron manema labarai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel