Kaico! An tsinci gawar wani bawan Allah a cikin kududufi

Kaico! An tsinci gawar wani bawan Allah a cikin kududufi

A yammacin ranar Alhamis ne aka tsinci gawar wani mutum mai matsakaicin shekaru a cikin wani kududufi da ke harabar gidan rediyo na gwamnatin na garin Asaba, babban birnin jihar Delta.

Wani shaidan ganin ido ya ce akwai alamar rauni a jikin gawar a yayin da aka ciro shi daga kududufin da harshen sa a waje wanda hakan ya sa ake tsamanin an kashe shi a wani wuri daban ne sannan aka jefa gawarsa cikin ruwan.

The Punch ta ruwaito cewa shaidan ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu wadanda suka kashe mutumin sunyi amfani da damar rashin tsaro da ake fama da shi a jihar ne suka jefa gawar a ruwa.

Kaico! An tsinci gawar wani bawan Allah a cikin kududufi

Kaico! An tsinci gawar wani bawan Allah a cikin kududufi
Source: Original

Sai dai wani shaidan ganin idon ya ce akwai yiwuwar ruwa ne ya ingizo gawar zuwa kududufin daga wani wuri daban.

DUBA WANNAN: Tsaro: Fulani za su taimaka wa 'yan sanda fatattakar 'yan bindiga - IGP

"Ruwan baya gudu amma akwai wani ruwa daban da ke gudana daga wani kwalbati da ya hade da kududufin a tsallaken titi. Mai yiwuwa ruwa ne ya ingizo gawar zuwa inda aka tsince shi," a cewarsa.

Wani ma'aikacin gidan rediyon ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun razana a lokacin da suka samu labarin cewar an tsinci gawa a kududufin da ke harabar wurin aikinsu.

Ma'aikacin da ya nemi a sakayya sunansa ya ce, mahukunta gidan rediyon sun sanar da 'yan sanda cikin gaggawa kuma 'yan sandan suka amsa kirar suka dauke gawar ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Onome Onuvughayeya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce tuni jami'ansu sun dauke gawar kuma sun fara bincike domin gano dalilin rasuwar mutumin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel