Sabon shugaban NYSC ya shiga ofis

Sabon shugaban NYSC ya shiga ofis

-Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim wanda shine sabon shugaban NYSC ya shiga ofis ranar Juma'a 3 ga watan Mayu, 2019

-Janar Shuaibu Ibrahim shine shugaban hukumar NYSC na 18 cikin shekaru 45 da kafa wannan hukuma

Sabon shugaban NYSC mai suna, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya shiga ofishinsa a ranar Juma’a 3 ga watan Mayu, 2019. Inda zai cigaba daga wurin da Manjo Janar Suleiman Kazaure ya tsaya.

An shirya wani taro na musamman domin tarbar sabon shugaban a cikin babban dakin taro na shelkwatar NYSC dake birnin Abuja.

Sabon shugaban NYSC ya shiga ofis

Shugaban NYSC; Brigediya Janar Shuaibu Ibrahim
Source: UGC

KU KARANTA:Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo

Adenike Adeyemi wacce itace Daraktan sashen labarai na hukumar NYSC ta bada wannan sanarwa inda take cewa, Janar Shuaibu Ibrahim shine shugaban hukumar NYSC na 18 kenan inda kuma hukumar NYSC a halin yanzu take da shekara 45.

Dan asalin jihar Nasarawa ne, yanada digiri na farko da kuma na biyu a fannin tarihi, kana kuma yayi karatunsa ne Jami’ar Jos da Filato tsakanin shekarar 1989 zuwa 1992.

Haka kuma ya zarce zuwa Jami’ar Abuja inda yayi digiri na uku wato PhD a fannin tarihin har ila yau a shekarar 2007.

Sabon shugaban NYSC ya rike mukamai da dama a cikin aikinsa day au tsawon sama da shekaru ashirin yana yi.

Daga cikin mukaman da ya rike akwai: Rajistara a Jami’ar Soji dake Biu, shugaban sashen karatun tarihi da kuma ilimin yaki na makarantar horar da sojoji (NDA) dake Kaduna, jami’in bincike mai zurfi a cibiyar bincike ta soji, mataikamin shugaban NYSC daga 1996 zuwa 1999, da dai sauransu.

Kwararren ma’aikacine kuma malami, a don haka Birgediya Janar Ibrahim Shuaibu ya buga littafai da dama inda kuma akwai wadanda aka kawo masa domin yin gyara a ciki.

Domin haka zai shigo wannan hukumar NYSC a shirye domin cigaba da daukaka martabar hukumar duba ga kwarewarsa da kuma aiki tukuru da ya jima yana yi tsawon rayuwarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel