An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna

An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna

-Kwara nada arzikin noma indai har gwamnati zatayi abinda ya dace a wannan bangaren, inji masana harkokin noma

-Ka kasance tamkar su Ahmadu Bello da Awolowo domin dawo da martabar jiharka, wasu kwararru sun shawarci AbdulRazaq AbdulRahman

Wasu kwararru sun shawarci zababben gwamnan Kwara da yayi koyi da Ahmadu Bello, Awolowo da sauran shugabannin da suka gabata wadanda suka jajirce wajen ganin Najeriya ta tsaya da kafafunta.

Wannan shawara ta biyo bayan hasashen da sukeyi na cewa jihar Kwara zata iya zama jiha wacce ake tinkaho da ita a fannin noma, musamman idan gwamnati ta maida hankali akan noma rani da wasu manyan ayyukan more rayuwa a jihar.

An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna

An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna
Source: UGC

KU KARANTA:Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo

Da suke magana wajen wani taron karawa juna sani na kwana biyu wanda kwamitin musayar gwamnati ta Kwara ta shirya, tace garin nada yelwar yin noma domin ciyar da kansu har ma su baiwa wasu daban amma fa idan anyi abinda ya dace.

Taron wanda aka sanyawa taken: Farfado da harkokin noma a Kwara, kwararru a wannan fanni wadanda suka fito daga wurare daban daban a fadin kasar nan sun yabawa AbdulRazaq bisa neman shawarar yadda za’a cinma wani manufa.

“ Kwara na da albarkar ruwa domin yin noma. Amma sai dai ba ayi kyakkyawan tanadi ba domin noman rani, da zarar ruwan sama ya tsaya shikenan noma zai tsaya. Ko shakka babu wannan ba karamar matsala bace saboda babu kasar da a fadin duniyan nan ta dogara da ruwan sama kadai wurin noma.

Ya zama wajibi Kwara ta bullo da tsare-tsare domin yin noman rani saboda ya kasance ana iya yin noman gaba daya shekara”. Kingley Olurinde ya fadi, wanda wani kwararre ne da cibiyar bincike mai zurfi kan harkokin nomad a cigaban karkara ta Illorin.

Wani kwararren shima mai suna Dr Sam Okunade ya baiwa AbdulRazaq shawarar cewa yayi koyi da irin salon mulkin Sardauna da Awolowo wadanda sukayi aiki tukuru domin ganin yankunan sun samu cigaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel