Mai a daidaita sahu ya kashe abokin aikinsa a Kano

Mai a daidaita sahu ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rundunar 'yan sanda na jihar Kano ta tabbatar da kama wani mai a daidaita sahu mai shekaru 19, Abu Hussain mazaunin Maidile Qiuaters da ake zargi da kashe abokin aikinsa Mansur Ibrahim.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan cikin wata sako da ya fitar a ranar Juma'a inda ya ce wanda ake zargin ya yi dabawa abokin aikinsa almakashi a kirjinsa ne kuma hakan ya yi sanadiyar rasuwar sa.

Kiyawa ya ce an tabbatar da rasuwar Murtala Mohammed ne a asibitin kwararu da aka kai shi domin yi masa magani kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mai a daidaita sahu ya kashe abokin aikinsa a Kano

Mai a daidaita sahu ya kashe abokin aikinsa a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun jihar Kano

Ya ce lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Mayun misalin karfe 2 na rana sakamakon rashin jituwa da ya faru tsakanin matasan biyu a gadan Kabuga.

"Sakamakon rashin jituwar da ya faru tsakanin su ne Hussain ya dabawa Mansur Ibrahim almakashi a kirjinsu kuma nan take aka garzaya dashi Asibitin Kwararu na Murtala Mohammed inda aka tabbatar ya rasu," inji Kakakin 'yan sandan.

Ya ce rundunar 'yan sandan ta fara bincike a kan lamarin, ya kara da cewa za a gabatar da wanda ake zargi a gaban kotu idan an kammala binciken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel