'Yan sanda sun fara binciken zargin yiwa karuwai fyade a Abuja

'Yan sanda sun fara binciken zargin yiwa karuwai fyade a Abuja

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta babban birnin tarayya, Abuja ta kafa kwamitin bincike na musamman domin duba zargin fyade da aka yiwa wasu jami'an ta.

An ce an gudanar da fyaden ne a ranar 27 ga watan Afrilu yayin da aka kama wasu da ake zargin masu aikata karuwanci yayin jami'an hukumar FCTA suka kai kai farmaki wani gidan rawa mai suna Caramelo.

Wasu daga cikin matan da aka kama sunyi ikirarin cewa an ci mutuncinsu, tare da dukkansu har ma da yin lalata da su.

'Yan sanda sun fara binciken zargin yiwa karuwai fyade a Abuja

'Yan sanda sun fara binciken zargin yiwa karuwai fyade a Abuja
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Tsaro: Fulani za su taimaka wa 'yan sanda fatattakar 'yan bindiga - IGP

Sunyi ikirarin cewa wasu daga cikin jami'in 'yan sanda da ke aiki ofisoshin 'yan sanda a Utako, Life Camp da Gwarimpa sunyi musu fyade.

Bayan wannan zargin ne mataimakin kakakin 'yan sanda, ASP Gajere Tanimu ya fitar da sanarwa a ranar Juma'a a Abuja inda ya ce rundunar ta aike gayyata ga wasu mutane da za su taimaka wurin binciken.

A yayin da ya ke tabbatar wa al'umma cewa hukumar ba za ta lumunce rashin da'a ba, Tanimu ya ce akwai hukuncin mai tsanani ga duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel