Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Femi Falana, shahararren lauyan nan na kare hakkin dan-adam, ya bukaci da a hana jigajigan ma'aikatan gwamnati musamman shugaban kasa da gwamnoni yawace-yawace zuwa kasashen ketare har sai an shawo kan tabarbarewar harkar tsaro.

Falana ya yi wannan jawabi ne yayin gabatar da wata kasida game da 'yanci da dokokin yada labarai.

"Lokaci ya yi da shugaban kasa da kuma ko wani gwamna wanda ke kasar ketare ya da ya dawo gida Najeriya don kula da harkar tsaro wanda ya ke da matukar muhimmaci a wannan lokaci". In ji shi.

Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun jihar Kano

Ya kara da cewa, "kasancewar muggan 'yan daba da ma su sace mutane don neman kudin fansa, da kuma 'yan ta'adda sun mamaye Kasar, ya zama dole a hana shugaban kasa da gwamnoni fita zuwa kasashen ketare har illa ma-sha-Allahu. kowa ya kuma san cewa tsabar talauci ne silan wadannan muggan ayyuka".

A game da rawar da kafafen yada labarai za su taka kan wannan lamari kuwa, Falana ya yi kira gare su da su mayar da hankali kan yadda za su karfafa gwiwan mahukuntan majalisu wurin kawo karshen wadannan matsaloli ta hanyar yin abun da ya kamata.

Idan ba a manta ba, a halin yanzun dai shugaban kasa muhammadu buhari ya na kasar Ingila a tafiyar kwanaki goma da zai yi wanda ba ya danganci aikin sa na shugabancin kasa ba ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel