Tsohon Ministan PDP ya musanta komawa jam'iyyar APC

Tsohon Ministan PDP ya musanta komawa jam'iyyar APC

An samu rudani a kan rahotan sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka ce tsohon Ministan Ayyuka, Sanata Adeseye Ogunlewe ya yi a Legas.

Duk da cewa kafafen yada labarai sun wallafa cewa ya fice daga jam'iyyar ta PDP, Sanatan ya shaidawa Daily Trust cewa yana nan daram dam a PDP.

Ya ce rahoton da aka wallafa na cewa ya fice daga jam'iyyar PDP labarin kanzon kurege na kawai.

Tsohon Ministan PDP ya musanta komawa jam'iyyar APC

Tsohon Ministan PDP ya musanta komawa jam'iyyar APC
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar mutane sunyi tsamanin cewa Ogunlewe zai fice daga jam'iyyar PDP ne duba da irin matsalolin da ya rika samu da shugabanin jam'iyyar na jihar Legas.

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Ogunlewe, wanda ya yi Ministan Ayyuka tsakanin 2003 zuwa 2006 karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana kin amincewarsa da nadin Dr Adegbola Dominic a matsayin shugaban PDP na jihar Legas bayan Moshood Salvador ya yi murabus.

Ya kuma soki yadda ake gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasa na Atiku Abubakar a yayin zaben 2019 da na dan takarar gwamna a jihar Legas, Jimi Agbaje.

Daily Trust ta ruwaito cewa ba a ga maciji tsakanin Ogunlewe da tsohon mataimakin jam'iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George wanda shine jagoran jam'iyyar PDP a jihar Legas.

Idan ba manta da dan Ogunlewe, Moyosore wadda ya yi takarar dan majalisa na mazabar Kosofo 1 jihar karkashin jam'iyyar PDP ya yi murabus daga jam'iyyar ya koma APC.

Sai dai a yayin da aka tuntube shi a jiya, Ogunlewe ya karyata rahotanin da ake yadawa na cewa ya fice daga jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel