Tsaro: Fulani za su taimaka wa 'yan sanda fatattakar 'yan bindiga - IGP

Tsaro: Fulani za su taimaka wa 'yan sanda fatattakar 'yan bindiga - IGP

Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya ce shugabanin Fulani a karkashin Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) sun amince za su tallafawa 'yan sanda domin fatattakar 'yan bindiga a jihar Kebbi da sauran sassan Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Danbazau, Sufeta Janar na 'yan sanda da wasu manyan jami'an gwamnati sun zaiyarci Kebbi bisa umurnin Shugaba Muhammadu Buhari domin su tattauna da shugabanin Fulani daga sassa daban na jihar a kan yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a ranar Juma'a bayan taron da su kayi, shugaban 'yan sandan ya ce, "Sun amince za su taimaka mana a yunkurin da mu na fatattakan 'yan bindiga daga jihar Kebbi."

Tsaro: Fulani za su taimakawa 'yan sanda fattakar 'yan bindiga - IGP

Tsaro: Fulani za su taimakawa 'yan sanda fattakar 'yan bindiga - IGP
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa

Ya kara da cewa ba dukkan 'yan bindiga a jihar bane 'yan kabilar Fulani.

Ya ce sun gana da shugabanin Fulani ne domin su san kallubalen da su ke fama da shi. "Za muyi kokarin yin sulhu da 'yan bindigan amma idan hakan ba ta yiwu ba za muyi maganinsu da karfi da yaji" inji IGP.

A baya, Ministan harkokin cikin gida da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu sun ce tawagar da shugaban kasa da ziyarci Kebbi bisa tsarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kirkiro da shi na tattaunawa da shugabanin Fulani a kan batun ta'addanci da 'yan bindiga ke aikatawa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel