'Yan sanda sun harbe wani matashi bai ji ba bai gani ba

'Yan sanda sun harbe wani matashi bai ji ba bai gani ba

- Jami'an 'yan sanda a jihar Taraba sun harbe wani matashi har lahira daga zuwa wurin kallon masu garkuwa da mutane da suka kamo

- 'Yan sandan sun harbe matashin a daidai kofar ofishin su lokacin da suke gabatar da wasu masu garkuwa da mutane da suka kamo

Jami'an 'yan sanda a jihar Taraba sun kashe wani mutumi da bai ji ba bai gani ba, mai suna Ure Boyi, a kusa da ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba ranar Laraba.

A rahotannin da majiyarmu LEGIT.NG ta samu ya nu na cewa mutumin ya mutu ne sanadiyyar wani harbi da jami'an 'yan sanda suka yi da niyyar su tarwatsa gungun mutane da suka taru a bakin kofar ofishin 'yan sandan domin su kalli wasu masu garkuwa da mutane da jami'an 'yan sandan suka kamo.

'Yan sanda sun harbe wani matashi bai ji ba bai gani ba

'Yan sanda sun harbe wani matashi bai ji ba bai gani ba
Source: UGC

Ba wannan ne karo na farko da aka fara samun irin wannan al'amari da jami'an 'yan sandan ba.

A watan Maris din da ya gabata ne wani jami'in dan sanda ya harbe wani saurayi a jihar Lagos, a lokacin da suke kokarin kama masu laifi, sai dai tuni hukumar 'yan sanda ta kasa ta dauki mataki akan jami'in dan sandan inda ta kore shi a aiki kuma ta danka shi a hannun kotu domin a yanke mishi hukunci.

KU KARANTA: An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

Hakazalika makon da ya gabata ne shugaban 'yan sanda na kasa ya ragewa dukkanin jami'an 'yan sandan Najeriya lokacin aiki daga awanni 12 zuwa awanni 8 a kowacce rana, shugaban ya yi hakane saboda ya bai wa jami'an 'yan sandan isasshen lokacin hutawa kafin su koma aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel