Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita

Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita

- Tarihi ya na nema ya maimaita kan shi, yayin da ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai samu damar dawowa daga tafiyar da ya yi ba ranar Lahadi nan

- Shugaban kasar ya kai ziyara kasar Birtaniya, inda fadar shugaban kasar ta bayyana tafiyar ta shi a matsayin ziyarar sirri

Akwai yiwuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai dawo Najeriya ba ranar Lahadi 5 ga watan Mayu, saboda zai tsaya a duba lafiyar sa.

Shugaban kasar zai cigaba da zama a birnin Landan din kamar yadda likitocinsa suka ba da umarni, a cewar jaridar Sahara Reporters.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Birtaniya a ranar 25 ga watan Afrilu, akan abinda fadar shugaban kasar ta bayyana a matsayin ziyara ta sirri.

Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita

Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita
Source: Depositphotos

A karo na farko kenan tun lokacin da ya zama shugaban kasa, Buhari ya ki sanar da 'yan Najeriya dalilin zuwan shi ziyara kasar Birtaniya, kuma ya ki rubuta wasika ga majalisar dokoki kasar domin sanar da su tafiyar ta sa, sannan kuma ya ki bayyana mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mai rikon kwarya.

Abinda shugaban kasar ya yi ya haifar da kace-nace a kasar, inda kundin tsarin mulki ya bayyana cewa a duk lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu ko kuma wani abu makamancin haka, dole ne ya rubuta takarda zuwa ga majalisar dokoki ya bayyana musu halin da ake ciki, sannan kuma ya bayyana musu cewa ya bai wa mataimakin sa rikon kwaryar shugabancin kasar.

KU KARANTA: An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

A wata tafiya da ya yi a shekarar 2017, a lokacin da ya jima bai dawo ba, masu zanga-zanga sun fito a birnin Lagos da Abuja da kuma kasar Birtaniya, inda suka bukaci shugaban kasar ya dawo gida ko kuma ya ajiye mulkin na shi, bayan da ya shafe sama da kwanaki 90 bai dawo ba.

Masu zanga-zangar sun shafe kwanaki uku suna gabatar da zanga-zangar akan gwamnati ta dauki mataki akan tafiyar shugaban kasar, saboda hakan zai iya zama illa ga kasar.

Zanga-zangar, wadda dan takarar shugaban kasa da ya sha kasa Omoyele Sowore, Charles Oputa da Deji Adeyanju suka jagoranta, ita ce ta tilasta shugaban kasar dawowa gida Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel