APC ta hadu da cikas yayinda kotu ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na Adamawa

APC ta hadu da cikas yayinda kotu ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na Adamawa

- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na jihar Adamawa, Abdulrauf Abdulkadir, kan bayar da bayanan karya ga hukumar INEC

- Justis Inyang Ekwo ya umurci APC da INEC ta gabatar da Mustapha Usman, wanda yazo na biyu a zaben fidda gwani da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoba, 2018, a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin kasar

- Usman yayi zargin cewa Modibbo ya bayar da shekarunsa na karya kuma bai cancanci takarar zaben fidda gwani na APC ba

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu ta hadu da cikas yayinda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori zababben dan majalisar wakilanta na jihar Adamawa, Abdulrauf Abdulkadir, kan bayar da bayanan karya ga hukumar INEC.

Justis Inyang Ekwo ya umurci APC da INEC ta gabatar da Mustapha Usman, wanda yazo na biyu a zaben fidda gwani da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoba, 2018, a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu a mazabar Yola ta kudu, Yola ta arewa, da Girei na jihar.

APC ta hadu da cikas yayinda kotu ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na Adamawa

APC ta hadu da cikas yayinda kotu ta dakatar da zababben dan majalisar wakilai na Adamawa
Source: Twitter

Kotun ta bayyana cewa Usman ya samar da laifin mallakar takardun makarantar firamare na Moddibo wanda suke na bogi da kuma shigarsa siyasa yayinda yake a matsayin dan bautar kasa wanda ya saba ma layi na na sashi 4 na dokar NYSC.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Yoba, ta umurci zababben dan majalisa na yankin Yola ta kudu, Yola ta arewa, da Girei, Abdurrauf Abubakar Modibbo ya sauka daga kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Wani jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Kotun ta umurci zababben dan majalisar ya sauka daga kujerarsa ya ba dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Jaafaru Sulaiman Ribadu.

Ribadu ne ya zo na biyu a zabe yan majalisar dokoki na ranar 23 ga watan Fabrairu a mazabar Yola ta kudu, Yola ta arewa, da Girei.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel