Mutane 540 Suka Rasa Ransu, 3, 383 Suka Jikkata a Hadurran Watan Janairu- In ji Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC)

Mutane 540 Suka Rasa Ransu, 3, 383 Suka Jikkata a Hadurran Watan Janairu- In ji Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC)

Mutane 540 ne suka rasa rayukkansu, wasu 3,383 suka jikkata a cikin hadurra 950 cikin watan Janairu a fadin kasar nan, in ji Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC). Kuma mutane 7,827 wadannan hadurran suka shafa.

A cikin wani rahoton wata-wata da hukumar take fitarwa kan hadurran hanya (RTC), wanda jami’in hukumar Corps Marshal Mr Baboye Oyeyemi ya sa ma hannu, kuma aka samar da shi ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, ranar jumu’a, yace yawan mutanen na nuna raguwar mace-mace da kashi 21 bisa dari.

Haka kuma rahoton na nuna raguwar afkuwar hadurra da kashi 14 bisa dari, da raguwar yawan mutanen dake jikkata da kashi 14 bisa dari idan aka yi la’akari da abunda ya faru a cikin watan Disamba.

KU KARANTA: Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

“Kididdigar hadurran da suka afku a cikin watan Janairu da na irinsa a shekarar 2018 na nuna kari a cikin kowane bangare.” Kamar yadda rahoton ya nuna, hanyar Legas zuwa Ibadan tafi yawan hadurra da kashi 57 dake matsayin raguwar kashi 11 bisa dari daga watan Disambar 2018.

“Hanyar Abuja zuwa Lokoja da ta Kaduna zuwa Abuja na biye da hadurra 54 da 51. Kididdigar da aka yi kan jihohi ta nuna cewa jihar Kaduna tana gaba da yawan hadurra har 95.

“Birnin Tarayya (FCT) na biye da hadurra 83, sai jihar Ogun wadda keda 64 da Nasarawa mai kashi 58 ita kuma Oyo tana da 46.”

A wani wajen kuma, yace Kaduna tafi samun yawan hasarar rayukka har 53 wato kashi 48 dake matsayin raguwa bisa ga yadda aka samu a watan Disambar 2018.

“Jihohin Bauchi da Ogun na biye a tsarin yawa da rasa rayukka 44 a kowace jiha, yayin da Kano da Oyo suke da 35 da 28.”

Rahoton ya nuna cewa karye dokar gudu ce umul’abasin afkuwar mafiyawancin hadurra da suka kai 502 a matsayin kashi 49.4 bisa dari na abubuwan dake haddasa hadari.

Motocin kasuwa keda kashi 65.5 bisa dari na yawan hadurran da aka samu a cikin watan da ake nazari. “Yayin da motocin gida keda kashi 32.7 bisa dari, su kuma motocin gwamnati keda kashi 1.8 bisa dari.

”Hukumar ta roki gwamnatin tarayya da kafofin watsa labarai masu zaman kansu da su taimaka wurin ilmantar da al’umma kan yadda ake amfani da hanya don kara fadakarwa ga masu amfani da hanya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel