Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo

Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo

-Bana son tsaiko cikin aikina saboda haka bazan aminta da hakan ba daga wajenku, Amaechi ya fadawa hukamar gudanar da layin dogo ta kasa.

-Aikin dake gabanmu na layin dogo daga Legas zuwa Ibadan ya kusa kammaluwa, inji Amaechi

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta gargadi sabbin mambobin hukumar kula da layin dogo (NRC) da kada suyi wani abu da zai kawo cikas a ayyukan da gwamnatin keyi na fannin layin dogo.

Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo

Layin dogo: Ba fa zaku kawo mana tsaiko ba, gwamnatin tarayya ta fadawa hukumar kula da layin dogo
Source: Facebook

KU KARANTA:N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi shine ya fadi wannan magana a shelkwatar ma’aikatar sufuri ta kasa dake Abuja, inda ake nadin sabbin mambobin NRC su ashirin.

Yace “ kun san duk inda aka hada kungiya kamar wannan dake da mutane sama da goma dole za’a rika samun sabanin fahimta da kuma ra’ayi. Duk da haka ina tunanin zaku hada kanku domin yin abinda yakamata.

“ Ba zan bar kowa ya kawo min tsaiko ba, ko shugaban kasa ma ya san da hakan. Ko da yake wa’adin mulkin ma yazo karshe daga ranar 29 ga watan Mayu babu wanda ya (daga cikin ministoci) sani ko shugaban kasa zai sake bashi damar kasancewa minista.” A fadar Amaechi.

Amaechi ya cigaba da cewa, “ Duk wanda zai kasance ministan sufuri kada ku kawo masa tsaiko saboda sashen sufuri na layin dogo na bukatar kulawa ta musamman. A yanzu haka muna kan aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan wanda muke sa ran zuwa karshe watan Mayu za’a kammala shi.” 

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel