Wani jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Wani jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Wani jigon jam’iyyar PDP, Sanata Adeseye, ya bayyana a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu cewa a shirye yake don barin jam’iyyar adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Ogunlewe, wanda ya kasance tsohon ministan ayyuka, ya tabbatar da lamarin ne a wani tattaunawa tare da manema labaran siyasa na Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Legas.

Yana martani ne akan sauya shekar da dansa, Moyosore yayi kwanan nan daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Motosore ya nemi takaran kujerar dan majalisan dokokin jihar Legas a karkashin jam’iyyar PDP inda ya sha kayi sannan ba da dadewa ba, ya bayyyana ra’ayin shi akan barin jam’iyyar.

Wani jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Wani jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
Source: UGC

Ya kasance mai halartan tattaunawan APC a yankin shi tare da sauran jiga-jigan APC har da Bayo Osinowo, mamban majalisan dokokin jihar kuma zababben sanata mai wakiltan mazaban yankin Gabashin Legas.

Ogunlewe ya bayyana ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa dansa wanda ya kasance lauya, ya sauya sheka zuwa APC sannan kuma nan da kwana 30 zai bi shi.

Tsohon ministan ya bayyana cewa har ila yau ya shiga APC ne saboda ya gamsu cewa jam’iyyar zata kasa shugabanci zuwa ga yankin Kudu a 2023 bayan haka jam’iyyar ta kasance mai tsari.

KU KARANTA KUMA: Yahaya Bello ya ajiye siyasa a gefe, yayi wa Dino ta’aziyyar mutuwar mahafiyarsa

Ogunlewe yace ba zai so a bar shi ba a baya a shirin baiwa yankin shugabancin 2023.

Yace zai bar PDP tare da magoya bayan shi, ya kuma yi alkawarin zai kara inganci ga jam’iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel