Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

-Sufeton yan sanda ya dakatar da jami'an yan sandan dake tsare wasu daidaikun mutane a kasar nan, saboda da yawansu basu cancanci hakan ba a cewarsa.

-Yanzu ba kowa bane yan sanda zasu rinka yiwa gadi, zance daga bakin Adamu Mohammed

A kudurin da babban sufeton yan sanda yake dashi na ganin cewa ba’a bambamta tsakanin yan Najeriya, Mohammed Adamu yace mutanen da basu cancanta ba, ba zasu sake samun yan sanda domin tsaronsu ba.

Adamu ya fadi wannan maganarce a shelkwatar yan sanda dake birnin tarayya Abuja ranar Alhamis yayinda da ake gudanar da taron manyan kwamandodin yan sanda.

Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane
Source: UGC

KU KARANTA:Wasu mutum 4 sun gurafana gaban kotu bisa laifin sakin karnukansu kan ‘yan sanda

Taron wanda makasudin yinsa shine domin sufeton ya samu ganawa da sabbin kwamandodin yan sanda da aka nada a runduna 67 dake fadin kasar nan wadanda zasu kula da yan sandan dake kaiwa da komowa.

“ Yanada matukar muhimmanci a inganta aikin yan sandan sintiri. Ana samun wurare da dama kaga wanda sam bai cancanci tsaro ko rakiya daga wurin yan sanda ba sai ka ganshi ana yi masa. Daga yanzu wannan abu ya kau.

“ Ya zama dole mu tabbatar da aldaci tsakanin yan kasa baki daya. A don haka ya zama wajibi ku bi dokokin aikin yan sanda domin yin aiki bisa abinda ya kamace ku.” Inji sufeton.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel