Yahaya Bello ya ajiye siyasa a gefe, yayi wa Dino ta’aziyyar mutuwar mahafiyarsa

Yahaya Bello ya ajiye siyasa a gefe, yayi wa Dino ta’aziyyar mutuwar mahafiyarsa

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yayi ta’aziyya ga sanata mai wakiltan yankin Kogi ta yamma, Dino Melaye, akan mutuwar mahaifiyarsa

- An sanar da mutuwar Deaconess Comfort Melaye a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu

- Ya bayyana marigayiyar a matsayin jajirtaciyyar uwa, mai riko da addinin Kirista kuma shugaba a garin wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen yiwa Allah da al’umma hidima

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello yayi ta’aziyya ga sanata mai wakiltan yankin Kogi ta yamma, Dino Melaye, akan mutuwar mahaifiyarsa, Deaconess Comfort Melaye wacce aka sanar da mutuwarta a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

A sakon ta’aziyya zuwa ga sanatan, Gwamna Bello ya bayyana labarin mutuwar Deaconess Melaye a matsayin “mai cike da jimami kuma babban rashi ba wai ga jihar Kogi kadai ba harma ga Najeriya baki daya, duba ga irin gudunmawar da ta bayar wajen ci gaban al’umma.”

Babban sakataren labaran gwamnan, Onogwu Muhammed ya gabatar da takardar ta’aziyyyar wanda ke dauke da sa hannun gwamnan ga Legit.ng.

Yahaya Bello ya ajiye siyasa a gefe, yayi wa Dino ta’aziyyar mutuwar mahafiyarsa
Yahaya Bello ya ajiye siyasa a gefe, yayi wa Dino ta’aziyyar mutuwar mahafiyarsa
Source: Facebook

Ya bayyana marigayiya Deaconess Melaye a matsayin “jajirtaciyyar uwa, mai riko da addinin Kirista kuma shugaba a garin wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen yiwa Allah da al’umma hidima.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An kashe mutane hudu a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma

“A madadin mutanen jihar Kogi, iyalaina dani kaina, ina mika ta’aziyyarmu gareku yayinda nake addu’an Allah ya ba ahlin gidan Melaye juriyan karban wannan rashi da suka yi,” gwamnan ya rubuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel