Yakin Neman Kujerar Kakakin Majalisa

Yakin Neman Kujerar Kakakin Majalisa

Yakin Neman Kujerar Kakakin Majalisa Wakilai: Gbajabiamila Ya Ba ‘Yan Majalisa Kyautar Wayoyin Salula

Dantakarar dake kan gaba kuma wanda jam’iyyar APC ta tsayar a takarar Kakakin Majalisar Dokoki zagaye na tara, Honorabul Femi Gbajiabiamila, a jiya ya fara yekuwar neman kujerar a lokacin da ya tara zababbin ‘yan majalisar wakilan da suka fito daga bangarorin siyasa daban-daban a Abuja don fada masu kudurinsa.

Bayan ya bayyana masu shirin da yake da shi kan zaben da za a yi na shugannin da za su gudanar da mulkin Majalisar Dokoki wanda za a yi a wata mai zuwa, Gbajiabiamila kuma ya raba ma zababbin ‘yan majalisar kyaututtuka.

Kafin a ba su kyaututtukan da suka hada da wayoyin salula, an bukaci manema labarai da su fita dakin taron na Chelsea Hotel dake Abuja. Alokacin da suka fita zuwa wani wurin da aka shirya taron manema labarai a cikin otel din, zababbin ‘yan majalisar sun karbi kunshin kyaututtukan da aka ba su, wadanda ke dauke da wayoyin salula kuma suka dauki hotuna daban-daban.

KU KARANTA: Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

Majiyoyi a wurin taron sirrin da aka gudanar sunce zababbin ‘yan majalisar sun sa hannu a kan wata rijista kafin su karbi wayoyin salular da wasu kayututtukan da aka sa a cikin ambulan. Majiyoyin sunki bayyana abubuwan dake cikin ambulan din da aka ba zababbin ‘yan majalisar.

LEADERSHIP ta ranar jumu’a tace, Gbajabiamila ne ya jagoranci taron da aka yi, inda yace a halin yanzu yana da goyon bayan zababbin ‘yan majalisar wakilai 178 daga dukkan manyan jam’iyyun siyasa dake da wakilci a majalisar. Kamar yadda abokan huldar siyasarsa suka ce, yawan mutanen ya isa yasa Gbajiabiamila samun nasarar cin kujerar shugabancin majalisar wakilan a lokacin da za a kaddamar da ita cikin watan Yuni mai zuwa

Daya daga cikin masu biyayya ga dantakarar Kakakin Majalisar Wakilan haifaffen Legas, Honorabul Onofiok Luke (dan jam’iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom), wanda ya gabatar da jawabi a wani taron manema labarai bayan tabbatar da goyon baya ga Gbajiabiamila, yace sun yanke shawarar goyon bayan ya samu kujerar saboda cancantar sa, da bude al’amari, da gogewa a cikin aikin majalisa. Honorabul Luke wanda Kakakin Majalisar Dokokin jihar Akwa Ibom ne mai barin gado, kuma zababben dan majalisar wakilai yace dukkan zababbin ‘yan majalisar wakilan 178 da suke goyon bayan Gbajiabiamila sun halarci taron kuma sun yanke shawarar su zabe shi saboda “dan majalisa ne da bai nuna bambancin bangare.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel