N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

-Mafi karancin albashin N30,000 ba zai ishe ma'aikatan Najeriya ba, inji Oricha

-Kungiyar kwadago ta nemi akara kudin daga N18,000 zuwa N56,000 amma gwamnatin tarayya ta barshi a N30,000

Shugaban kungiyar ma’aikatan sashen lafiya na asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja, Steve Oricha yace N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta kaddamar ba zai canja rayuwar ma’aikata ba.

Oricha wanda ya zanta da wakilinmu ranar Alhamis a Gwagwalada yace duk cewa sabon mafi karancin albashi abu ne mai kyau amma sai dai ba zai taimaki ma’aikata ba.

N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba
Source: UGC

KU KARANTA:Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura

Yace “ a nawa ganin ba na tunanin gwamnati tayiwa ma’aikata abin yabawa bisa maida mafi karancin albashi zuwa N30,000.”

Ya sake cewa, kungiyar kwadago ta kasa ta nemi a sanya mafi karancin albashin ya kasance N56,000 sai kuma gwamnati bata amince bat a barshi a N30,000. A ganinsa wannan kudin ba zai kauda matsalolin ma’aikatan Najeriya ba.

Har wa yau, lokacin da da mafi karancin albashin ke N18,000 dalar Amurka tana daidai ne da N170 amma a yanzu N350 shine ke daidai da dala guda. “Don haka babu wani canji da N30,000 zata kawo a rayuwar ma’aikatan Najeriya.” Kamar yadda Oricha ya fadi.

Oricha ya kara da cewa, kulli yaumin a kasar nan farashi abubuwa hawa sama suke ba batun sauka. Idan kuwa akwai irin wannan abu a kasar nan sabon mafi karancin albashin babu abinda zai yiwa ma’aikata saboda ba isarsu zaiyi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel