Wasu mutum 4 sun gurafana gaban kotu bisa laifin sakin karnukansu kan ‘yan sanda

Wasu mutum 4 sun gurafana gaban kotu bisa laifin sakin karnukansu kan ‘yan sanda

-Wasu mutane sun sakowa yan sanda karnuka harma sun cijesu a Abuja

-Da gangan mutanen suka aikata wannan laifi ba wai bisa kuskure ba

A ranar Alhamis 2 ga watan Mayu ne aka gurfanar da wasu mutum 4 gaban kotun Mpape dake birnin Abuja akan laifin sake karnuka kan jami’an yan sanda.

Yan sanda sun cafke mutanen masu suna, Patrick Anyafulu, Iluobe Kester, Kennedy Victor da kuma Aseogua Oritsebenigho wadanda suke zaune a shiyyar Poli-Macus Estate Gwarinpa da laifin muzgunawa da kuma hana jami’ai yin aikinsu.

Wasu mutum 4 sun gurafana gaban kotu bisa laifin sakin karnukansu ga ‘yan sanda

Wasu mutum 4 sun gurafana gaban kotu bisa laifin sakin karnukansu ga ‘yan sanda
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura

Wanda ya shigar da karar, Stanley Nwaforaku yace a ranar 9 ga watan Afrilu yayinda yan sanda karkashin umurmin babban sufetonsu ke gudanar da wani bincike akan masu garkuwa da mutane suka shiga unguwar wadannan mutane domin suyi kame.

A cewarsa yan sanda sun wuce zuwa gida mai lamba 30 wanda ke bisa titin Isah Khalid a Poli-Macus Estate Gwarinpa domin kama wadanda suke nema.

A daidai lokacinda jami’an yan sandan suka gabatar da kansu a matsayin jami’ai dake da izini kama masu laifin. Kwatsam sai suka turo masu da karnuka da gan-gan. Har ma karnuka sun ciji yan sandan.

Wannan laifin ya sabawa doka ta sashe na 97, 149, 267 da kuma 246 karkashin dokar Penal Code.

Bayan da mai karar ya gama karanta jawabin karar nan take wadanda ake tuhuma suka amshi laifin nasu ba tareda gardama ba.

Alkalin kotun ya sanya masu tara naira 200,000 a matsayin beli. A karshe kuma ya dage sauraron wannan kara zuwa 24 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel