Yanzu-yanzu: An kashe mutane hudu a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma

Yanzu-yanzu: An kashe mutane hudu a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma

- An kaure da wani mummunan rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Ogun

- Rikicin ya samo asali ne yayin da wasu makiyaya suka kora shanunsu cikin wani kogi domin su sha ruwa, sanadiyyar hakan ruwan kogin ya lalace

Wani mummunan rikici da ya kaure a garin Iwoye da ke karamar hukumar Imeko-Afon jihar Ogun, tsakanin wasu makiyaya da manoma.

An yi asarar rayukan mutane hudu sanadiyyar rikicin wanda ya faru jiya Alhamis 2 ga watan Mayu.

Wani bincike kuma ya nuna cewa wani jami'in hukumar 'yan sanda na yankin Imeko da kuma Inspector na hukumar an harbe su sanadiyyar rikicin.

Yanzu-yanzu: An kashe mutane hudu a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma

Yanzu-yanzu: An kashe mutane hudu a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma
Source: UGC

Majiyarmu LEGIT.NG ta fahimci cewa rikicin ya samo asali ne bayan da wasu makiyaya suka kora shanunsu domin su sha ruwa a wani kogi da ke yankin, inda suka gurbata ruwan.

Mun samu rahoton cewa, wani wanda ya yi kokarin ya yi wa makiyayan magana sun harbe shi a take a wurin.

Jami'an 'yan sanda da suka yi kokarin ganin sun shawo kan matsalar abin ya ci tura, inda wasu makiyaya da suka yi kwanton bauna suka budewa jami'an 'yan sandan wuta suka kashe mutum daya.

KU KARANTA: An kashe mutane biyu a wurin biki a jihar Nasarawa

Mutumin da aka kashe an bayyana sunan shi da Kabiru Ogunrinde.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ya zuwa yanzu dai sun samu rahoton mutuwar mutum daya.

Ya ce, "Ba su kama kowa ba har yanzu. Sannan 'yan sandan da suka ji rauni an garzaya da su zuwa asibiti."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel