'Yan shi'a sun gabatar da shaidar cewa Zakzaky ya makance

'Yan shi'a sun gabatar da shaidar cewa Zakzaky ya makance

- 'Yan shi'a sun gabatarwa da kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya wasu shaidu da ke nuna cewa shugaban su Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya makance a idon sa na hagu

- 'Yan shi'ar sun bayyana cewa a harin da sojoji su kai wa malamin a gidan sa da ke Zaria a shekarar 2015, lokacin ne sojojin suka harbe shi a idon sa na hagu

'Yan kungiyar 'yan uwa musulmai wadanda aka fi sani da 'yan Shi'a, sun gabatar da wani hoto da ya ke nuna shaidar cewa shugabansu Ibrahim El-Zakzaky ya samu matsala a idonshi.

'Yan kungiyar sun gabatar da tsohon hotunan El-Zakzaky lokacin da yake gani da kyau da kuma hoton shi na yanzu da ya samu matsalar idon bangaren hagu, ga kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, a lokacin da suke gabatar da wata zanga-zanga a Abuja jiya Alhamis.

'Yan shi'a sun gabatar da shaidar cewa Zakzaky ya makance

'Yan shi'a sun gabatar da shaidar cewa Zakzaky ya makance
Source: Facebook

Sakataren kungiyar, Abdullahi Mohammed Musa ya ce ziyarar da kungiyar likitoci da kuma wasu daga cikin 'yan kungiyar kare hakkin dan adam suka kai wa malamin ta tona asirin gwamnatin tarayya akan cin zarafin da ta ke yiwa malamin.

KU KARANTA: Wani dan sanda ya maka abokinshi a kotu saboda ya kasa yiwa matarsa ciki, wanda ya basu damar kwanciya har sau 77

Ya bayyana cewa, jami'an tsaro sun harbe shi a idonsa na hannun hagu, inda idon ya fito a lokacin da suka kai musu hari gidan sa dake Zaria a shekarar 2015.

Ya ce suna gabatar da zanga-zangar ne dauke da hotunan malamin lokacin da aka harbe shi a ido, wanda hakan ke nu ni da cewa malamin yana bukatar taimakon gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel