Yan bindiga: Majalisar wakilai tayi na’am da cikakken aikin sojoji a jihar Katsina

Yan bindiga: Majalisar wakilai tayi na’am da cikakken aikin sojoji a jihar Katsina

- Majalisar wakilai, a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, ta umurci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta baci a wasu yankuna a jihar Katsina

- Hakan ya biyo bayan wani batu da Ahmed Safana ya gabatar kan bukatar gwamnati ta sanya baki a kisan kiyashin da ake wa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba

- Safana ya kuma yi korafi akan lalata dukiyoyi da yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ke yi a yankin

Majalisar wakilai a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, ta umurci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta baci a mazabar Safana/Batsari/Dan Musa da ke jihar Katsina, da kuma tura sojoji a yankin domin duba ayyukan yan ta’adda a mazabar.

Hakan ya biyo bayan wani batu da Ahmed Safana ya gabatar kan bukatar gwamnati ta sanya baki a kisan kiyashin da ake wa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba, da kuma lalata dukiyoyi da yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ke yi a yankin.

A cewar jaridar Daily Sun, Safana, a muhawararsa, ya sanar da majalisar cewa garuruwa da dama a mazabar na karkashin harin yan bindaga da muggan makamai a yanzu haka.

Yan bindiga: Majalisar wakilai tayi na’am da cikakken aikin sojoji a jihar Katsina

Yan bindiga: Majalisar wakilai tayi na’am da cikakken aikin sojoji a jihar Katsina
Source: Depositphotos

Dan majalisan ya kuma bayyana cewa yan bindigan na aiki da dare da kuma rana tsaka, suna kashe mutane da kuma sace mutane.

Yace abun bakin ciki ne ganin kashe-kashen na ci gaba yayinda hukumomin tsaro basu tabuka komai ba, duk da bayanai daga mambobin garuruwan da abun ya shafa.

Da suke tofa albarkacin bakinsu a muhawarar, mambobin majalisar sun nuna damuwa kan tabarbarewar lamarin tsaro a kasar, inda suka bayyana cewa babu wani yanki na kasar da ya tsira.

KU KARANTA KUMA: Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar

Yan majalisan sun bayyana cewa yawan fashi da makami, sace-sacen mutane da karya doka a fadin kasar gazawar bangaren zartarwa ne, wacce ke kula da hukumomin tsaro, domin su gudanar da ayyukansu.

Bashir Baballe, yace akwai bukatar majalisa ta sanya baki tare da bangaren zartarwa kan lamarin tsaro a kasar, kafin wa’adin majalisa na takwas ya kare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel