Kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai: ‘Yan Asalin Delta da Edo dake Kasashen Ketare Mabiya APC Sun Aminta da Omo-Agege

Kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai: ‘Yan Asalin Delta da Edo dake Kasashen Ketare Mabiya APC Sun Aminta da Omo-Agege

A lokacin da ‘yan majalisar dattijai zagaye na tara ke fuskantar zaben sabbin jami’an da za su jagoranci al’amurran majalisar, ’yan jam’iyyar APC a jihohin Delta da Edo dake zaune a kasashen ketare suna neman aba nasu kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar.

Kuma sun roki shugabannin jam’iyyar da su yi abunda ake bukata ta hanyar gabatar da Barista Ovie Omo-Agege a matsayin amintaccen dantakarar kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, dayake cikin hikimar jam’iyyar ta sadaukar da kujerar ga yankin Kudu maso kudu.

A wani bayani shugabannin kungiyar ta‘yan asalin jihohin na Delta da Edo mazauna kasashen ketare, Princely Ovakpo dake wakiltar kabilun Urhobo, da Anioma, da ljaws, da sauransu, da kuma Nosa Obaobowha, wanda ke wakiltar Binis, Ishan, Akoko-Edo, Ugbogi da sauransu, sunce goya ma Omo-Agege baya zai yaukaka zumuncin dake akwai a tsakanin bangaren majalisa da mulki.

Suka ce a irin wannan lokaci da dimokaradiyyar kasar nan ke fuskantar babban kalubalen shugabanci daga jam’iyyar hamayya, yana da muhimmanci cewa irin Sanata Omo-Agege dake da himma da cikakkar biyayya ga jam’iyya za a bari ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai.

KU KARANTA: Karancin lebarori daga kasashen waje zai kawo sauyin farashin abinci, inji Manoma

Suka kara da cewa “ya kamata APC ta yi cikakken nazari ta bar jarumi kuma dan majalisar dake da azancin zance, masanin sha’anin majalisa, wanda bai bada kai ga ‘yan hamayya ya samu alhakin shugabanci irin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, ba wai wani wanda bai iya bada kariya ga jam’iyyarsa ba. "

“Don haka muna muna kira ga Shugaban kasa da shugabannin jam’iyya da su aminta da bukatarmu ta hanyar tabbatar da an ba Omo-Agege damar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai don shugabanci mai dorewa da zaman lafiya, wannan ita ce bukatarmu bayan nasarar da shugabanmu Shugaban kasa Buhari ya samu."

“An jarraba Omo-Agege kuma an same shi daya daga cikin masu biyayya ga zababben shugaban kasa, don haka idan an zabi irin wannan mutum ya yi aiki da Shugaban Majalisa, shugaban kasa zai iya bacci da ido biyu, ganin irin yadda yayi fada a lokutta da dama don kare dokar da ta shafi sha’anonin zabe."

“Ba mu shakkar cewa idan aka ba shi wannan damar, zai cika gibin dake tsakanin sashen majalisa da sashen mulki da kyakkyawar mu’amala da za ta kawo cikakken cigaba a fadin wannan kasar, don haka muke mika wannan bukatar ga shugabannin jam’iyya da su bada wannan damar."

“Muna da cikakkiyar masaniya cewa ta hanyar ba shi kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, ta’asar da ‘yan bindiga ke tafkawa za ta zama tarihi, samun dan asalin Neja Delta irin Omo-Agege zai tabbatar da nakkasa ayukkansu, dayake shi ya fito daga yankin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel