Fashin Offa: An dage sauraron kara, saboda 'yan bindiga sun rufe hanyar da za a shigo da shaida

Fashin Offa: An dage sauraron kara, saboda 'yan bindiga sun rufe hanyar da za a shigo da shaida

- Rashin zuwan shaida kotu ya tilasta dage shari'ar 'yan fashin Offa, saboda 'yan bindiga sun rufe hanyar da za a fito da shaida daga jihar Zamfara a kawo shi jihar Kwara domin bayar da shaida

- An dage karar ne har zuwa ranar 6 ga watan Yuni

An samu akasi a wurin cigaba da sauraron karar 'yan fashin da aka kama na Offa, saboda rashin zuwan wanda zai bayar da shaida kotu.

Mutane biyar din da ake zargi, Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salahudeen Azeez da kuma Niyi Ogundiran, ana tuhumar su akan, ta'addanci, kisan kai da kuma fashi da makami.

A lokacin da ake sauraron karar da aka gabatar a gaban kotun jihar Kwara jiya Alhamis, alkalin kotun mai shari'a Haleema Salman, da babban mai gabatar da kara Farfesa Wahab Egbewole (SAN), ya bayyanawa kotu cewa rikicin jihar Zamfara na 'yan bindiga shine ya hana mai bayar da shaidar zuwa garin na Ilorin.

Fashin Offa: An dage sauraron kara, saboda 'yan bindiga sun rufe hanyar da za a shigo da shaida

Fashin Offa: An dage sauraron kara, saboda 'yan bindiga sun rufe hanyar da za a shigo da shaida
Source: Depositphotos

Ya roki kotu ta daga karar har zuwa wani lokaci.

Mai kare wadanda ake kara Mathias Emeribe bai yi wani tsokaci akan hakan ba.

Mai sharia Salman a ranar 8 ga watan Afrilu ta daga sauraron karar akan wadanda ake zargin zuwa jiya Alhamis.

KU KARANTA: An kama wadanda suka sace Hakimin Daura

Masu kawo kara da wadanda ake kara, sun samu sabani akan maganganun da wadanda ake tuhumar suka yi, inda masu kare masu laifin suka bayyana cewa an tilasta wadanda ake tuhumar ne wurin amsa laifinsu, saboda haka ba za ayi amfani da wannan bayanin a matsayin shaida ba.

Tuni, kotun ta aika da bayanin ciwon da wanda ake tuhumar zuwa ga likitoci domin gabatar da bincike a kai.

A karshe dai alkalin kotun mai shari'a Haleema Salman ta dage sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel