Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar

Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar

Kotun kolin kasar Saudiyya ta yi kira ga dukkanin Musulmi da su nemi jaririn water Ramadan a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu sannan su sanar da kotu mafi kusa game da wadanda suka ga watan ido da ido ko kuma ta abun hangen nesa, kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ta ruwaito.

Kotun kolin ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, yayinda ake sanya ran fara azumin watan Ramadana a ranar Lahadi sannan a ci gaba har zuwa farkon watan Yuni.

A tsakanin wannan wata guda Musulmi a fadin duniya kan kame bakinsu daga ci da sha tun daga billowar alfijir har zuwa ga faduwar rana.

Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar

Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar
Source: UGC

Watan Ramadana ya kansace wata mai tsarki wanda a cikinta Musulmi kan dukufa tare da kara kaimi wajen ibada da kuma komawa ga mahallicinsu domin samun falalar da ke kunshe da wannan wata mai albarka.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya yaba da nadin dan Najeriya a matsayin minista a kasar Kanada

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Kwamitin gudanarwa ta Masallacin mai alfarma Sarkin Musulmi Bello dake garin Kaduna, wanda aka fi san da suna Sultan Bello ta sanar da soke sallar Tahajjud da ibadar I’itikafi a azumin watan Ramadan bana.

Kaakakin kwamitin, Adamu Lawal Mijinyawa ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, inda yace kwamitin Masallacin Sultan Bello ta yanke wannan shawara ne bayan wani zama da yayanta suka yi a karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Sa’idu Aliyu Kakangi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel