Atiku ya yaba da nadin dan Najeriya a matsayin minista a kasar Kanada

Atiku ya yaba da nadin dan Najeriya a matsayin minista a kasar Kanada

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a zaben da ya gudana, kuma tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jinjina wa Mista Kaycee Madu, dan Najeriya na farko da aka zaba a matsayin dan majalisa a Alberta, kasar Kanada, sannan kuma aka nada shi a matsayin ministan harkokin birni.

A wani jawabi da Atiku ya saki da kansa yace ya gay an Najeriya na samun ci gaba a Najeriya, dama fadin duniya, sannan cewa wannan shine burinsa a koda yaushe.

Ya kara da cewa nasarorin da Mista Madu ya samu a gida da waje, zai sauya daukar da kasashen duniya ke yiwa Najeriya, wanda a shekarun baya sun fuskanci wasu kalubale.

Atiku ya yaba da nadin dan Najeriya a matsayin minista a kasar Kanada

Atiku ya yaba da nadin dan Najeriya a matsayin minista a kasar Kanada
Source: UGC

“Sannan abu mafi muhimmanci, ya zama dole mu duba rawar ganin da ilimi ya taka wajen nasarar Mista Madu. Kamar yadda na fadi a baya, ilimi shine hannun jari da ke haifar da riba mafi girma. Na san cewa, na zuba kudina a inda bakina yake.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro ne ke tsotse mana albarkatunmu – Buhari

“Iya yadda Najeriya ta zuba jari a ilimi, iya yadda mutanenmu za su zamo cikin haske, a gida da waje.

“A yau ina jinjinawa nasarorin Mista Madu. Ina alfahari da kai kuma zai yi iya bakin kokarina don tabbatar da cewa Ahmadu da dama da Gbenga da dama da Emeka da dama sun bi sahun ka,” inji Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel