Domin tsaro ba don tsoro ba: Babu sallar Tahajjud babu Ittikafi a Masallacin Sultan Bello

Domin tsaro ba don tsoro ba: Babu sallar Tahajjud babu Ittikafi a Masallacin Sultan Bello

Kwamitin gudanarwa ta Masallacin mai alfarma Sarkin Musulmi Bello dake garin Kaduna, wanda aka fi san da suna Sultan Bello ta sanar da soke sallar Tahajjud da ibadar I’itikafi a azumin watan Ramadan bana.

Kaakakin kwamitin, Adamu Lawal Mijinyawa ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, inda yace kwamitin Masallacin Sultan Bello ta yanke wannan shawara ne bayan wani zama da yayanta suka yi a karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Sa’idu Aliyu Kakangi.

KU KARANTA: Sabon salo: Buhari yayi sabbin nade nade guda 26 daga Landan

Domin tsaro ba don tsoro ba: Babu sallar Tahajjud babu Ittikafi a Masallacin Sultan Bello

Masallacin Sultan Bello
Source: UGC

Legit.ng ta ruwaito daga ciki wadanda suka halarci wannan zama har da babban Malamin dake gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai tsarki a Masallacin a duk watan Ramadan, Dakta Ahmad Abubkar Mahmud Gumi.

“Muna taya duk ilahirin Musulmai murnar zuwan wata mai albarka, watan Azumin Ramadan, kuma muna kira ga kowa da zauna lafiya, hakanan mu kasance masu lura da tsaron lafiyarmu data dukiyarmu.

“Za’a fara tafsirin bana a ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu da misalin karfe 4 na rana, amma sakamakon matsalar tsaro da ake fuskanta, kwamitin ta soke gudanar da Sallar Tahajjud a Masallacin a yayin Ramadan, haka zalika kwamitin ta soke ibadar Iikitafi a azumin bana.” Inji shi.

Daga karshe kwamitin ta nemi Musulmai dasu yi hakuri da wannan mataki data dauka, sa’annan tayi kira a garesu da suyi mata kyakkyawar fahimta sakamakon halin da ake ciki ne yasa daukan wannan mataki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel